Labarai

Wani Ɗalibi Ya Kashe Abokin Karatunsa A Katsina Ta Hanyar Zuba Mashi Maganin Ɓera A Cikin Fura Ya sanya Gawarsa Rijiya

A ranar Talatar nan ne rundunar ƴan sanda ta jihar Katsina ta gabatar da wani mutum mai suna Laminu Saminu ɗan asalin ƙaramar hukumar Mani da laifin kashe wani abokinsa jami’in rundunar tsaron farin kaya ta Sibil difens (NSCDC).majiryarmu ta samu wannan rahoto daga wani marubucin Muhammad Aminu Kabir da ya wallafa a Shsfinsa na facebook

Kakakin rundunar SP Isah Gambo ne ya gabatar da mai laifin ga manema labarai a shelkwatar ƴan sandan da ke Katsina.

SP Gambo ya ce a ranar 26 ga watan Satumban da ya gabata, Laminu Saminu ya kashe abokin na sa mai suna Sunusi Bawa bayan da ya ziyarci gidansa da nufin duba shi ya ga ko lafiya tunda ya kira wayarsa har sau 11 amma bai ɗaga ba.

Wani Ɗalibi Ya Kashe Abokin Karatunsa A Katsina Ta Hanyar Zuba Mashi Maganin Ɓera A Cikin Fura Ya sanya Gawarsa Rijiya
Wani Ɗalibi Ya Kashe Abokin Karatunsa A Katsina Ta Hanyar Zuba Mashi Maganin Ɓera A Cikin Fura Ya sanya Gawarsa Rijiya

Marigayi Sunusi Bawa yana da muƙamin mataimakin Sifuritanda na rundunar Sibil difens da ke Katsina kuma ya je ne gidan abokin nasa da niyar ya ziyarce shi inda anan kuma abokin nasa ya kashe shi ya binne gawarsa a rijiya.

Ƴan sanda sun ce yadda aka yi asirin Laminu ya tonu shi ne, bayan an ɗan ƙwana biyu da kashe abokin nashi sai ya ƙirawo matar mamacin ya ce mata jami’an Kwastan sun kama mota sai an kawo takardu inda ya faɗa mata cewa ta duba cikin Mashin akwai takardun zai zo ya karɓe su, to amma kasancewar matar ta ga ba ma ta mota su ke ba ana cikin tashin hankalin mijin ta ne amma kuma shi gashi yana maganar takardun mota don haka sai ta yanke shawarar ta sanar da ƴan sanda kuma aka ci sa’ar kamashi bayan gudanar da bincike ya amsa cewa shi ne ya kashe abokin nashi.

Da ana tambayarsa yadda aka yi ya kashe shi sai ya ce, “Sunusi ya zo gidana ne don ya duba ni ya ga ko ina lafiya tunda ya kirawo wayarta har kusa sau 11 amma ban daga ba, to da ya zo ne bayan mun gaisa ya ce man ina ta kiran wayarka baka ɗauka ba sai na ce mashi ban gani ba da ya ke na sanya ta caji ne, daga nan sai na ce mashi ya zo mu je wani gida da na kama ma wani abokina haya, to da muka je sai na buɗe ma shi gareji ya sanya motar shi saboda baya son yara su gogar mashi mota, bayan mun shiga gidan sai na fito don in samo mashi abinci, da na je ban samu abinci ba sai na sanya aka dama ma shi fura daga nan ne wata zuciya ta raya man in sanya mashi maganin ɓera a ciki shine na saya na sanya na bashi ya sha.” Inji Laminu.

Ya ci gaba da cewa, ” bayan ya sha furar da maganin ɓeran ne sai ya fara galabaita ni kuma sai na ɗauko wani icce na buga mashi a kai da ya mutu na sanya gawar rijiya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button