Labarai

Sakkwato da Yobe ne su ka lashe gasar karatun Kur’ani ta ƙasa karo na 37

Wakilin Jihar Sakkwato, Nura Abdullahi da ta Jihar Yobe, Aishatu Abdulmutallib ne su ka yi nasarar lashe gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 37 da aka gudanar a Gusau, Jihar Zamfara.

Wanda ya yi nasara a bangaren maza Nura Abdullahi ya samu kambun gwarzon shekara daga Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar. Kamar yadda Daily Nigerian Hausa na ruwaito

Sakkwato da Yobe ne su ka lashe gasar karatun Kur’ani ta ƙasa karo na 37
Sakkwato da Yobe ne su ka lashe gasar karatun Kur’ani ta ƙasa karo na 37

Hakazalika, Aishatu Abdulmutallib ta bangaren mata ta samu lambar yabo ta tauraruwar bana daga uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Aisha Mattawalle a wajen bikin rufe gasar da aka yi a Gusau a jiya Asabar.

Da ya ke sanar da sakamakon gasar, Shugaban kwamitin, Farfesa Yalwa ya ce wanda ya zo na ɗaya a ɓangaren maza, Abdullahi ne ya yi nasara da maki 97.9, sai Abdullahi Sadiqu-Sadiq daga jihar Zamfara da maki 96.9 a matsayi na biyu, Salish Abdullahi na jihar Neja ya zo na uku da maki 95.9.

Muhammed Kabir na Kebbi ya zo na hudu da maki 94.7, Faruk Kabir na jihar Kano ya zo na biyar da maki 94.0 Usmanu Abubakar ya zo na shida a gasar.

Shugaban ya kuma bayyana sakamakon ajin mata kamar haka; Aisha Abdulmutallib ta Yobe da maki 96.4 da Maimuna Hussaini daga FCT da maki 94.1.

Haka kuma Aisha Kabir ta jihar Gombe ta zo matsayi na uku da maki 93.5 sai kuma Zainab Habib ta jihar Kano a matsayi na hudu da maki 92.9.

Sauran sun hada da: Fatima Mustapha daga jihar Kaduna ta zo ta biyar da maki 92.5, yayin da ta shida Fatima Ahmad ta jihar Nasarawa da maki 92.3.

A nasa jawabin shugaban taron kuma Sarkin Wase a Jihar Nasarawa, Alhaji Jibirin Bala ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da lokacinsu wajen karantarwa da haddar Alkur’ani mai girma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button