Kannywood

Rarara Ya Gwangwaje Ango Lukman da Amaryar sa da Sabuwar Mota, Dj ma an masa ruwan Nairori

Kamar dai Yadda Aka sani a ranar Asabar dinda tagabata ne aka daura Auren fitaccen Jarumi a Masana’antar shirya Finafinan Hausa Yusuf Saseen Wanda Akafi Sani da Lukman Acikin Shiri me dogon Zango labarina.

An daura Auren ne a garin Patiskum ta Jahar yobe inda wannan daurin Aure ya samu hakartar manyan jarumai, produsoshi, masu bada umurni da dai sauran su, acikin jaruman Kannywood da suka halarci wannan daurin Aure an hango Darakta malam Aminu Saira, Yaseen Auwal, Isah perozkhan, Nasir naba , Babbale hayatu da dai sauran su.

Rarara Ya Gwangwaje Ango Lukman da Amaryar sa da Sabuwar Mota, Dj ma an masa ruwan Nairori
Rarara Ya Gwangwaje Ango Lukman da Amaryar sa da Sabuwar Mota, Dj ma an masa ruwan Nairori

A bangaren mata Jarumai kuma an hango Fuskar Jaruma Saratu Gidado, Maryam yahaya, Hadiza Saima, Aisha Humaira da sauran su.

A wurin Shagalin Bikin dinner ne aka Hango Fuskar mawaki rarara inda yayi jawabi na minti biyu Kamar yadda yayi Alkawari, domin tun kafin bikin ma yayi Alkawarin cewa indai lokacin yayi to tabbas Zai halarci wurin taron wanda hakan yasa yacika Alkawarin sa.

A lokacin da yake jawabi ne Sai dj ya saka wakar da Rararan yayiwa Zababben dan Takarar shugaban Kasar Nigeriaba Jam’iyyar APC watau Bola Ahmed Tinubu sannan kuma ya roki rarara daya bashi kyautar mota, amma dai hakan bata samu sai dai yace zai basu dubu hamsin hamsin shida MC.

A Kyautar da rararar yayiwa Ango da Amaryar sa kuwa Ya bayyana cewa Zasu karba ne ta hannun mataimakiyar sa watau Aisha Humaira wanda kuma ana Kyautata Zaton cewa Mota ce ya basu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button