Mahaifiyar Bola Tinubu ta kasa Zama a kasar ne London domin bata Jin sautin Kiran Sallah ~Cewar Sheikh Kabiru Gombe
A wani gajeran Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumintar zamani an hango sheikh Kabir Gombe Yana bayyana Darajojin Mahaifiyar Tsohon Gwamnan jihar lagos Kuma Dan takarar neman Shugabancin Nageriya a karkashin jam’iyar APC Mai Mulki.


Gombe Yana Mai cewa a Lokacin da suka ziyararci Bola Tinubu a jihar lagos bayan Mahaifiyar sa ta rasu Sheikh Abdullahi Bala lau yayiwa Tinubu wa azi inda ya kwadaita Masa irin romon dake cikin sadakatul-jariya cewa yanzu tunda Mahaifiyar sa Allah ya karbi ranta to abinda zaiyi shine ya Gina mata rijiyoyi ko masallatai amatsayin Allah ya Kai ka’dan kabarinta. Jaridarmikiya na ruwaito
Ga bidiyon nan nan ku saurara.
Sai Bola Tinubu ya bude baki yayi godiya ga kungiyar izalah kasancewar itace kungiyar addini daya tilo daga Arewa wacce ta kai masa ziyara domin jajantawa bisa rashin Mahaifiyar sa Bola Tinubu yace hakika ba karamin Rashi yayi ba domin duk Lokacin Aikin hajji Dana Umara Lokacin azumin Ramadana Mahaifiyar sa tana rubuto Masa sunayen mutun dari uku da nufin ya kai su kasa Mai tsarki makkah domin badar allah.
Har asibitin ciwon Ido tasa ya Gina a lagos domin ta hango irinsa a kasar waje Kuma Babu shi a Nageriya duk domin talakawa su Sami damar jinya ba tare da zuwa kasar waje ba.
Sheikh Gombe ya Kara da cewa Mahaifiyar Bola Tinubu ta gaza Zama a kasar London ne sakamakon rashin Jin Kiran Sallah domin ita ba zata iya Zama a wajen da Bata Jin sautin Kiran Sallah ba inji shi.
Da alama dai kungiyar izalah Bola Tinubu zata goyi baya a zaben na 2023.
Bola Tinubu Dan takarar neman Shugabancin Nageriya yanzu Haka Yana auren mata daya Kuma ita da ‘ya ‘yan duk sun kasance mabiya Addinin kiristanci.