Kungiyoyin kare Hakkin Dan Adam sun koka kan yadda Yiwa mata kaciya ya samu gindin zama a Najeriya
Wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun koka kan yadda kaciya ga mata ya cigaba da samun wurin zama a Najeriya.
Kungiyoyin sun koka da haka ne a taron wayar da kan mutane sannin illolin dake tattare da yi wa mata kaciya da kungiya Mai zaman kanta ‘Trailblazer’s Initiative Nigeria (TBI)’ ta shiyar tare da hadin gwiwar Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya UNICEF a Ibadan ranar Laraba. na ruwaito
Shugaban kungiyar TBI Dare Adaramoye ya ce alkaluman da UNICEF ta fitar sun nuna cewa har yanzu akwai mata da dama da ake yi wa kachiya a jihar Oyo.
Adaramoye ya ce duk da cewa a shekarun da suka gabata an samu raguwa a yawan matan da ake yi wa kachiya, har yanzu yanzu ana yi wa mata da yawa kaciya a jihar.
Ya ce akwai wasu al’adu da mutane suka yadda da su wanda ke sa ba za su iya bari ba idan suka haifi ‘ya’ya.
“ Ba gaskiya bane cewa yi wa mace kachiya na hana ta neman maza ba amma tarbiyyar ta gari daga wajen iyaye ne ke hana hakan faruwa. Yi wa mace kachiya na daga cikin hanyoyin tauye wa mace hakkinta.
Ya ce yi wa mata kaciya na haifar da matsaloli da suka hada da yoyin fitsari, samun matsaloli a duk lokacin da mace take ganin jinin ta na wata-wata, samun matsaloli wajen haihuwa, jin zafi a lokacin jima’I da dai sauran su.
A nata tsokacin shugaban kungiyar musulmai mata ta Najeriya (FOMWAN) Airat Ogungbenro dake Ibadan ta ce kamata ya yi a Kai taron wayar da kan mutane illan Yi wa mata kachiya zuwa karkara a jihar Oyo.
Ogungbenro wace itace tsohuwar shugaban hukumar kare hakkin yara ta jihar Oyo CPN ta Yi kira ga mata da su yi gaggawan Kai kara ga jami’an tsaro a duk lokacin da aka tilasta su su bada ‘ya’yan su mata domin yi musu kachiya.
“Muna bukatan matan da aka yi wa kachiya su fito su bayyana ilollin suke fama da su a dalilin kaciyar da aka Yi musu.
“Yi wa mace kachiya na tauye hakkinta mata a kasar nan.