Labarai

Kotu ta yanke wa tsohon ɗan Hisbah hukuncin rataya bisa laifin kashe budurwarsa

Wata kotu a jihar Kano, mai zaman ta a Miller Road, ƙarƙashin jagorancin Amina Adamu ta yanke wa wani Dayyabu Muhammad, tsohon ma’aikacin Hisbah, hukuncin kisa ta Hanyar rataya bisa samun shi da laifin kashe budurwarsa.

Kotu ta yanke wa tsohon ɗan Hisbah hukuncin rataya bisa laifin kashe budurwarsa
Kotu ta yanke wa tsohon ɗan Hisbah hukuncin rataya bisa laifin kashe budurwarsa

Kotun ta kama Muhammad da laifin kashe Hauwa Ibrahim, ta hanyar caccaka mata wuƙa tana kwance a dakin ta a unguwarsu a Daily Nigerian Hausa na ruwaito

Mai Shari’a Amina Adamu ta ce yanke wa Muhammadu hukuncin kisan ke bayan da ta gamsu da hujjojin da shaidun mai ƙara su ka gabatar.

Tun da fari, an zargi Muhammad ne da kashe Hauwa bayan ta nuna ba ta son shi da aure kamar yadda ya nema.

Shi Muhammad, kamar yadda ɗan uwan marigayiyar ya bayyana, almajirin gidansu ne, inda daga bisani ya nuna yana son ta aure Ita kuma ta ƙi amincewa da shi, sannan iyayen ta su ka goya mata baya.

Yayan nata ya ƙara da cewa jin haushin ƙin amincewar da shi ne ya sanya kwatsam wata rana, sai ji aka yi Muhammad ya kutsa kai cikin dakin ta tana kwance ya riƙa luma mata wuƙa, inda kafin a yi wata-wata, ta ce ga garinku nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button