Labarai

Kisan Ummita: Alkali ya sake kiran mahaifiyar Ummukulsum da ɗan sanda

A yau Juma’a ne wata babbar kotun Kano ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta dawo da mahaifiyar Ummulkulsum, Fatima Zubairu da PC Aminu Halilu domin sake yi musu tambayoyi kan zargin kisan da wani dan kasar China, Frank Geng Quangrong, mai shekaru 47 ya aikata a kan ƴarta.

Ana tuhumar Frank, wanda ke zaune a Railway Quarters a Kano da laifin kisan kai, kuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga Satumba, a Janbulo Quarters ,Karamar Hukumar Gwale a Kano.

Kisan Ummita: Alkali ya sake kiran mahaifiyar Ummukulsum da ɗan sanda
Kisan Ummita: Alkali ya sake kiran mahaifiyar Ummukulsum da ɗan sanda

Ana zarginsa da daɓa wa Ummulkulsum, wacce aka fi sani da Ummita, mai shekaru 22 wuka a unguwar Janbulo da ke Kano.

Lauyan da kare Quanrong, Muhammed Dan’azumi ya roki kotun da ta sake kirawo mahaifiyar Ummulkulsum da kuma ɗan sanda Halilu domin a sake yi musu tambayoyi, kamar yadda sashe na 258 na kundin dokar laifuka, ACJL, ya bada dama.

ACJL ya ce “kodayaushe kotu na iya kiran shaidu ko kuma ta kira shaidu don bincike da sake bincikarsu idan ana ganin suna da mahimmanci ga shari’a.

Dan’azumi ya kuma yi rokon kotu ta gayyaci babban daraktan lafiya ko babban jami’in kula da lafiya na asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ya gurfana a gaban kotun.

Ya roki kotu da ta amince da wannan rokon nasa.

Ibrahim Arif Garba, lauyan masu shigar da kara bai yi suka a kan hakan ba.

Bayan sauraron dukkan bangarorin biyu, Alkalin kotun, Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya amince da rokon sake kiran shedu da babban daraktan lafiya ko babban jami’in kula da lafiya na asibitin kwararru na Murtala Muhammed da su gurfana a gaban kotu.

Ma’aji ya ɗage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 11 ga watan Janairu da kuma 12 ga watan Janairu domin jin shaidun kariya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button