Labarai

Ina Bukatar Mijin Aure, Ban Son Na Mutu Ban Yi Aure Ba: Kyakkyawar Budurwa Ta Koka A Bidiyo

Wata budurwa ta daura bidiyo a manhajar TikTok tana kokawa kan yadda har yanzu bata samu mijin aure ba.

Ina Bukatar Mijin Aure, Ban Son Na Mutu Ban Yi Aure Ba: Kyakkyawar Budurwa Ta Koka A Bidiyo
Ina Bukatar Mijin Aure, Ban Son Na Mutu Ban Yi Aure Ba: Kyakkyawar Budurwa Ta Koka A Bidiyo

A gajeren bidiyon da budurwar mai suna Amrah ta daura, ta bayyana cewa babbar manufarta a rayuwa shine ta wayi gari a dakin mijinta

Amrah ta godewa Allah bisa wayen gari lafiya kuma a matsayin Musulma amma dai tace gaskiyar magana itace mace na bukatar aure.legit na ruwaito

Ta ce duk kudin mace a duniyar nan babbar manufarta itace shiga gidan aure.

Ta ce ita dai ta kosa ta shiga gidan miji kuma ta kosa ta sallamawa mijinta kafin ta mutu.

Tace:

Assalamu Alaikum, gaskiya abin tausayi ne na waye gari sabon wata a gidan miji na ba. Na ji maganganu masu dadi da mara dai akan aure amma nima ina son ayi da ni, ina son sallawa mijina.”

“Amma dai na godewa Allah da ya tashe da lafiya kuma Musulma. Maganar gaskiya shine rashin aure ga mace abin bakin ciki ne. Babbar manufar mace shine gidan aure, ku manta da maganganun masu ikirarin yancin mata.”
“Gaskiya ban son na mutu ba tare da nayi aure ba.”

Jama’a sun yi magana kan bidiyon:

 

@baby..amrah I honestly do not want to die without experiencing what marriage life feels like…Not married, Is this something I should be scared of ???????????? #babyamrah #islamicjourney_ #notmarried ♬ original sound – Islamic Reminders ????

Martanin Mutane 

Aminu Yusuf KN yace:

Allah ya azzurtaki da mijin aure nagari abin tunkaho Allahumma Ameen Yarabbil Alameen Oh’Lord, Oh’Lord, Oh’Lord.”

Shamsu Muhd Abubakar:

Idan Ta Yarda Bbu Lefe Toh Gobe Nazo A Daura”
Naseer Rabi’u:

Tazo Mu Rufawa Juna Asiri.. Na Bata Pi Network A Matsayin Sadaki”
Abubakar Umar:

“Allah zabamiki miji nagari me tsoron Allah ameen”
Auwal Bello Abin Godiya:

Allah yakawo mafita Allah yakawo nagari AMIN Allah yakarawa shugabamu fiyayen halita anabbi muhmmaduh rasulilahin s a w daraja AMIN”
Abubakar Umar yace:

Allah zabamiki miji nagari me tsoron Allah ameen

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button