Labarai

Hotuna: Ba za daɗe ba mutane za su koma masu ƙusumbi saboda yawan amfani da wayar salula

Masu bincike sun gano yadda nan kusa mutane za su sauya yanayin kirarsu saboda yawan amfani da abubuwan da fasahar zamani ta kawo, Labarunhausa na ruwaito.

Za su koma wata siffa mai suna “Mindy” wacce wuyanta ya dara na mutane kauri, ga kusumbi sai kuma karamar kwakwalwa.

Siffar Mindy taba da ban tsoro kuma akwai yuwuwar mutane su koma haka nan gaba kadan bisa binciken Toll Free Forwarding. Kakakin yace:

Fasaha ta sauya mana hanyoyin neman kudin. Mu na samun damar amfani da abubuwan da fasaha ta kawo har da wadanda ke iya shiga aljihunmu, ko kuma ince akwai damar yin sana’o’i ta wayar salula. Lallai fasaha ta kawo abubuwa da dama kuma babu alamar za a tsaya da gano sabbin abubuwa.

Yayin da fasaha ke ta samar da ayyuka, cigaba da ilimomi, akwai kuma yadda take sauya kira da halittar dan Adam.”

Ya bayyana cewa dan Adam na da saurin amsar sauyi, hakan zai bayar da damar canjawarsa a hankali daga wata surar zuwa wata.

Hotuna: Ba za daɗe ba mutane za su koma masu ƙusumbi saboda yawan amfani da salula
Hotuna: Ba za daɗe ba mutane za su koma masu ƙusumbi saboda yawan amfani da salula

Ya ce masu amfanin da wayar salula da kwamfuta su na iya sauyawa a yanayin zaman su.

Musamman wurin kallon fuskar waya ko kwamfutar, wajibi ne mutum ya rakwafa. Ya ce yayin rike waya, idan mutum zai kula zai gane yadda ya ke kwalmada kafadarsa ko da kuwa wurin dannata ko amsa waya ne.

Sannan a hankali wuyan mutum yana kwalmadewa ba tare da ya kula ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button