Hanyoyi 10 Da Zaki Iya Kaucewa Yin Zina Da Wanda Zai Aureki
Tabbas ko bincike na kimiya ya tabbatar da cewa masoyan da sukayi aure ba tare da yin zina kamin auren nasu ba sun fi wadanda suka taba yi samun zaman lafiya a aurensu.
Wasu matan ba a son ransu suke fadawa yin zina da wadanda zasu aura ba. Sai dai rashin yin zinar kamin aure shi yafi koda kuwa masoyin naki zai aureki idan yayi zinar dake.
Ga wasu hanyoyin da zaki iya kaucewa fadawa yin zina kamin aure da wanda zai aureki.
1: Yiwa Allah Alkawari: Tun farko ki yiwa Allah alkawarin cewa bazakiyi zina da duk wani namijin daya turo miki ya aureki ba.
Duk wani Musulmi dai yasan girman yiwa mutum alkawari bare kuma Allah (SWT) da kanSa.
Wannan alkawarin a kullum kika tunashi zai rika tsoratar dake ya kuma hanaki fadawa yin zina da manemin aurenki.
2: Ki Cire A Rai: ita zina tana soma yin tasiri ne daga lokacinda mutum ya soma tunanin ta ko ya saka ta arai.
Kwatakwata kada kiyi tunanin ko sha’awar yin zina da wanda zai aureki. Kawai burinki da tunaninki ya kasance bayan daura aure. Rashin saka tunanin yin hakan a rai zai taimaka miki wajen aikatawa.
3: Kula Da Kalamanki: Kada ki kuskura ki rika yiwa wanda zaki aura hiran batsa, haka shima kada ki bashi fuskar ya miki.
Kalamai na batsa sukan motsa mace ta soma sha’awar ganin abubuwan da suke tattaunawa sun kasance a zahiri. Don haka ki kauce yin hiran batsa da wanda zaki aura.
4: Gujewa Abubuwan Motsa Sha’awa: Duk wani abunda kikasan zai motsa miki sha’awa har ki soma tunanin yin zina da wanda zaki aura ki kiyaye shi.
Muddin zaki shiga kallon finafinai ko hutuna na batsa zaki motsa sha’awar ki. Motsawa kanki sha’awa kuma zai jawo ki soma tunanin Jima’i. Da zaran kin soma tunanin Jima’i wanda zaki so yin zinar da shi bai wuce wanda zaki aura ba. Hakan yasa kaucewa wadannan abubuwan sun zama dole muddin dai kina gudun yin zina da wanda zaki aura.
5: Ziyara: Kuskure ne budurwa ta rika ziyaran gida ko dakin wanda zai aureta.
Baya ga hakan zai iya jawowa kuyi zina, ziyaran wanda zai aureki zubda mutunci ne a matsayinki ta mace don haka duk yadda kike son namiji kada ki rika zuwa inda yake.
6: Kadaicewa: Idan har da gaske kike na bakison yin zina da namijin da zai aureki to ki guji Kadaicewa da shi.
Shi kadaici yakan jawo masoya su soma taba junansu ganin babu kowa tare dasu. Daga hakan kuma komai na iya faruwa.
Kiyi kokarin haduwa da mai sonki cikin mutane ko kuma inda mutane suke yawan gilmawa idan bazaki zo da ‘yan rakiya ba. Duk wani yanayin da kikasan zai kadaitaki da wanda zai aureki ki guje shi.
7: Guji Rokon Kudi: Kada ki kasance mai yawan neman bukatu ko kudi a wajen wanda zai aureki. Bayaga zubda mutunci da hakan yake jawowa, yana sa namiji ya soma sha’awar nemanki da zina maimakon zancen aurenki gudun kada ki auri wani ba shi ba.
8: Guji Shan Magunguna: Wasu yan matan sunada karambanin shan magungunar mata masu motsa musu sha’awa. Kada ki kuskura kiyi wannan gangancin domin yin hakan zai sa da kanki kije ki nemi mai son naki da aure saboda matsuwarki.
9: Mannewa Namiji: Muddin kika shaku da namijin da zaki aura to a gaskiya komai na iya faruwa a tsakaninku.
Kada ki bari ki saba da wanda zaki aura sabonda zai sa kiji kina iya yin komai saboda shi.
10: Ki Dubi Darajarki: Ki saka a ranki mutuncinki da darajarki yafi komai a wajenki. Hakan zai sa ki kauce baiwa namijin da zai aureki kanki.
Wasu matan sukan dauka gabansu ba wani daraja ne ko mutunci ne da shi saboda mai zasu hana mai bukata bare kuma wanda zai auresu. Wannan ba haka bane. Kinada matukar daraja a wajen namijin da bai sanki ta hanyar zina ba. Don haka ki saka a ranki gabanki shine mutuncinki
Wadannan abubuwan muddin ‘yan mata budurwai da basuyi aure ba zasu yi amfani dasu za a samu sauki zina kamin aure da asakarin masoya suke yi kamin aure.
Allah Ya bada ikon tsallake wannan matsayin ga duk wata mace mai burin ganin tayi aure ba tare da zina ba.