Labarai

Duk Wata Mace Ta Tsani Wadannan Abubuwan

Da akwai abubuwan da zaka iya yiwa mace su ta hakura. Da akwai kuma wasu abubuwan da duk yadda mace take sonka da zaka mata su koda wasa ne sai anyi dagaske zaku shirya.
Irin wadannan abubuwan kuwa sun hada da:

1: Cin Amana: Duk wata mace ko ta aure ko ta soyayya muddin har ta fahimci mijinta ko mai sonta yana neman matan banza, abunda na matukar bata mata rai.
Daga wannan lokacin kuma an rika samun matsala, hakan zai iya bijiro da rashin yarda da mijin ko saurayin.
2: Tsinkata Cikin Mutane: Akwai mazan da rashin mutuncinsu ya kai suna iya yiwa matansu ko wacce zasu aura wulakanci a gaban mutane ko kuma a cikin mutane.

Duk Wata Mace Ta Tsani Wadannan Abubuwan
Duk Wata Mace Ta Tsani Wadannan Abubuwan

Wannan rashin mutuncin da wasu mazan suke yi ba karamin cutar da wacce aka yiwa hakan yake yi ba. Wannan yasa duk wata mace ta tsani namiji ya tsinkata cikin mutane.
3: Rashin Daukanta Da Mahimmanci: Akwai mazan da suke ganin cewa tamkar alfarma suke yiwa mace idan sun aureta ko suke shirin aurenta. Hakan yasa basa ganin macen da suke tare da daraja ko mahimmanci.

Irin wadannan mazan suna iya furtawa mace kowani irin kalaman daya fito daga bakinsu na rashin daraja da girmamawa. Hakan yasa duk wata mace a fadin duniyan nan, ta tsani namiji ya nuna mata da ita da banza duk daya ne.

4: Rashin Bata Lokacin: Mata da dama ka basu lokacinka yafi ka basu kudinka.
Mace tanason taga mai sonta ko mai aurenta yana da lokacinta na musamman da bai barin wani abunda zai hanashi ganinta ko zama da ita. Hakan yasa duk wata mace ta tsani namiji ya hanata lokaci.
5: Nuna Wata Ta Fita: Idan kana son ganin bacin ran mace nan take nuna mata wata ta fita a wani fanni.
Mata sun tsani namiji ya ambatar musu wata da nufin ta fita da wani abun koda kuwa hakan ne.

Yanada kyau maza su fahimci cewa su fa Mata nutanene na musamman da suke bukatar kulawa na musamman.
Ba daidai bane namiji ya rika yiwa mace cin fuska ba kawai saboda ya fahimci tana sonsa. Idan har baka son mace ka rabuda ita cikin mutunci da girmamawa domin kaima kanada macen da kake burin a darajata.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button