Dr Muhammad Sani Umar R/lemo Yayi Tsokaci akan Hukuncin Da anka yankewa Abduljabbar
Babban shehin malamin addinin Muslunci Dr Muhammad Sani Umar R/lemo yayi tsokaci akan yadda yankewa Abduljabbar kabara hukuncin kisa bisa hanyar rataya saboda zagin Sahabbai da aibanta janibin Annabi Muhammad (s.a.w) ga kadan daga cikin abubuwan da shehin babban malamin ya fadi
” Hukuncin da kotu ta yanke jiya ga mutumin da ya shahara a garin nan wajen ɓacin shabban Annabi Muhammad (s.a.w) da al’amarin yayi nisa har yakai ga taba Annabi Muhammad (s.a.w) da iyalan gidansa da furta kalmomi migayu marasa dadin ji kuma yana cewa karantawa yayi a littafe Allah (S.W.T) ya nuna masa ayyarsa aka titsiye shi a bainar jama’a duk duniya ta gani anka ce litattafan da kake karantawa da kace kake karanta ya fadi sunanyen litattafan da shafi da lamba bude ka karanta.
Dr Muhammad Sani Umar R/lemo Yayi Tsokaci akan Hukuncin Da anka yankewa AbduljabbarAka shafe awanni mutumin nan ya kasa nuna ko daya tunda babu su shi yake kirkirarsu babu zagin shi ya kirkire shi kuma ya jingina ga Annabi Muhammad (s.a.w) wannan maganganu har duniya ta nade bazai ga wadannan Maganganu ba yace a Buhari yace a musulm sama da shekara dubu yana yawo hannun Musulmi sun masa hidima ba kadan ba.
Bayan Alkur’ani babu littafin da ankayiwa hidima kamar littafin sahihu Buhari sa’an sahihu Muslim gabascin duniya da yammacin duniya a hannunsa yake kuma musulman nan masoya ne ga Annabi Muhammad (s.a.w) ya zaga dinga dauko manya manyan laifukan kalamai na fyade na cin mutuncin da zina duk a litattafan nan kace Annabi yayi kuma mutane sun dauki shekaru sama da dubu suna karantar da wadannan littattafai har a gidanku an karantar da su amma basu ga zargin ba sai yanzu ko tsalakewa sukayi sai yanzu ka gani?.
Da yake ramen karya kurare ne babu inda zai je an shafe sama da shekara daya ana bibiyarsa da ya kare kansa abu mai samu ba kaga babu abinda alkali zaiyi face ya yanke hukuncin Allah babu wata abinda zaiyi sai wannan shekara daya sa rabi anka baka nan kace minti goma sunyi kadan yanzu an baka amma dama ance nuna gurin amma ya kasa nuna wurin dan babu abinda babu bazaka iya nuna shi ba.”
Wannan kadan ne daga cikin hudubar malam ga bidiyo nan sai a saurara.