Labarai

Dalilan Da Suke Saka Azzakarinka Yake Rigaka Miƙewa Duk Safiya – Bincike

Nocturnal Penile Tumescence (NPT). Wanda aka fi sani da suna Morning wood a turance, shine mikewar azzakarin duk safiyar Allah ga maza.

Wannan al’amarin yana faruwa ne ga dukkannin wani namiji, sai dai yafi faruwa da yara, zuwa matasa.
Suma manyan da suka haura shekaru 40 zuwa sama da haihuwa suna yin wannan lamarin na miƙewar azzakarin duk safiya.
Ba kamar yadda wasu suka fahimta ba na cewa hakan na faruwa ne idan namiji yana sha’awar yin Jima’i ko kuma yana son yayi fitsari. Idan wannan shine abunda kake tunani game da miƙewar azzakari da safe to ba wannan dalilan bane.
Yara maza ƙanana hatta jarirai idan da za a kula za a fahimci sukanyi wannan miƙewar gaban ba tare da sun yi fitsari ba. Don haka ba manufar miƙewar ba kenan.

Akwai wasu dalilai na halitta da Allah Ya halicci maza da hakan.
Mace idan aka ganta ta farka a jiƙe, kodai tayi mafarki ko kuma kamin tayi bacci sha’awa ya motsa mata da har ta jiƙa kayanta amma ba lokacin da take bacci ta jiƙa ba kamar yadda azzakarin maza yake miƙewa suna tsaka da bacci basu ma sani ba.
Wasu mazan sukan ji matukar kunya idan suka tashi suka fahimci gabansu ya rigasu tashi. Wanda hakan sai ya hanasu tashi daga inda suke har sai ya sace. Wasu mazan kuwa abun alfahari ne a wajen su na tabbatarwa na tare dasu mazantakan su.
Meke Jawo Miƙewar Gaban Namiji Da Safe? Wannan shine tambayar da zamu amsa a wannan darasin da dalilai kamar haka.
Sai dai su kansu likitoci basu haƙiƙance akan wannan binciken da suka yi, sune ainihin amsar da ya kamata su bayar ba gameda miƙewar azzakari da safe.
Sai dai sun gano cewa wasu abubuwan da suke sa hakan sun hada da:Dalilan Da Suke Saka Azzakarinka Yake Rigaka Miƙewa Duk Safiya - Bincike

1: Wasanni Kamin Kwanciyar Bacci: Duk da yake mutum ya kwanta bacci, idanuwansa suna rufe. Sai dai gangar jikinsa yana dawowa da abubuwan da suka faru da namiji kamin ya kwanta. Idan misali kamin namiji ya kwanta yayi wasa da matarsa ko wata can da har gabansa ya mike. Masana suka ce idan ya kwanta jikinsa zai dawo da wannan abun da ya faru kamin kwanciyar bacci sai kuma gabansa ya sake miƙewa gal ya tsaya tamkar idanuwansa biyu kuma ba mafarki yake yi ba.
Sukace wannan yana ɗaya daga cikin dalilan dake jawo azzakari namiji ya miƙe idan yana bacci.

2: Motsawan Hanyoyin Jini Da Ruwa: Duk safiya na Allah ma’ajiyar maniyinka yafi kowani lokaci gudana. Don haka da kayi motsi na alamun miƙewa. A wannan lokacin jinin jikinka yana zagayawa jikinka da sauri fiye da lokacin da bana motsa jiki ba. Don haka kamin ma ka mike tuni jini ya shiga ma’ajiyar maniyinka ya miƙar maka da Azzakarinka tun kamin kai ka mike daga kwance.
Sai dai shi wannan ma’ajiyar mani wato testosterone, ƙarfinsa na raguwa wani lokacin ga mazan da suka haura shekaru 40 zuwa 50. Don haka ba lalle bane ya miƙar musu da gabansu duk safiya kamar yadda zai iya yiwa ‘yan kasa da wannan shekarun, inji masana.

3: Samun Natsuwar Kwakwaluwa: A lokacin da mutum yake bacci, ƙwaƙwaluwansa na samun natsuwa da hutu. A wannan lokacin jini yana gudana duk ilahirin jikin mutum. Ga maza, daga lokacin da asuba ya daso wannan jini zai soma ƙwarara ne zuwa jijiyoyin gaban namiji, nan take gabansa zai miƙe, sannan zai ji yana jin fitsari. Ba fitsarin bane ya miƙar masa da gabansa ba, shi gaban ne miƙewarsa ya jawo masa jin fitsari saboda yadda sanyi wannan lokacin ya shiga jikinsa ya canza masa yanayin jikinsa idan yana yanayi na dumi zai dawo yayi sanyi, idan kuma sanyi yake zai ƙara jin sanyi sosai, don haka miƙewar gaban sa sai kuma fitsari ya biyo baya saboda sanyin da ya bugi fatar jikinsa koda a kasa mai yanayin sayi ko zafi yake. Ko a rufe da jikinsa yake ko a bude. Domin shi sanyi na asuba sanyi ne da masana suka ce na musamman ne saboda wasu dalilai ga yanayin rayuwar Dan Adam, Kwari da sirai duk muna amfana da sanyi asuba.
Ba kamar yadda wasu ke tunanin cewa saboda zasu yi fitsari yasa gabansu yake miƙewa da safe ko kuma suna sha’awar Jima’i ne ba. Sam babu guda daga cikin biyun nan kamar yadda binciken likitocin ya nuna musu.
Binciken nasu ya kuma tabbatar da cewa duk dare azzakarin maza yakan miƙe kamar sau 3 zuwa 5 ba tare da suna sha’awar Jima’i ba. Haka nan siddan.

Gaban na iya mikewa ya tsaya cak yana kaɗawa har na tsawon mintuna 30 har fiye ma, mai wusiyar bai ma san abunda yake faruwa ba. Amma da zaran ya farka daga bacci da ‘yan mintuna sai kuma gaban nasa ya kwanta.
Wannan Miƙewar Gaban Namiji Da Safe, kowani namiji ya kamata ace yana yin haka daga shekaru 6 da haihuwa har zuwa 70. Domin hakan yana alamta lafiyan da jinin namiji yake da shi a jikinsa zuwa hanyar gudanar jini zuwa gabansa.

Da zaran namiji ya fahimci cewa gabansa ya daina miƙewa da safe kamar yadda yake yi a baya musamman kuma yana da ƙarancin shekaru na haihuwa. Hakan na alamta cewa akwai matsalar kwararan jini zuwa wusiyar sa kenan. Da alamun zai iya kamuwa da cutar rashin ƙarfin gaba, ko mutuwar gaba da ake kira da harshen Nasara, Erectile Dysfunction (ED).

Maza masu cutuka irinsu Hawan jini, Ciwon shuga, ciwon Damuwa da yawan kitsai a jiki, suna iya kamuwa da wannan cutar na Erectile Dysfunction (ED) da zai raunana musu azzakarinsu koma ya kashe musu shi gaba ɗaya.
Muddin kana da sauran shekaru amma da safe kana riga Azzakarinka tashi daga bacci, yana da kyau ka tuntuɓi likita domin duba lafiyar buranka.
Sai dai abun fahimta anan bafa kowa ne yake yi haka duk safiya ba. Wasu sukan yi hakan duk bayan kwanaki biyu zuwa uku. Akwai ma masu yi mako mako. Hakan yana nuna yadda kake da ƙarfi da lafiyan gaba, haka zaka riƙa ganin gabanka na miƙewa duk safiya. Iya lafiyarka iya yawan mikewarsa.
Idan ka fahimci akwai sauyi daga abunda ka sani na mikewar, anan ne ya kamata ka nemi ganin likita ko irinsu Ustaz Usman U Usman domin su taimaka maka.
Da fatan za a kula da gabanka yadda ya kamata domin samun ƙarfin a ci gaba idomin samun ci gaba, idan ana da aure ko bayan anyi aure.
Allah Ya ƙara mana lafiyan gaba. Ya kuma kiyashe mu daga yin abun kunyar da gaban mu zai iya jawo mana.
#TsangayarMalam

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button