Labarai

Budurwa ta faɗa tarkon soyayyar wani boka, ta wallafa bidiyonsu tare suna soyayya

Advertisment

Wata budurwa ta janyo caccaka ko ta ina a kafafen sada zumuntar zamani bayan wallafa labarin soyayyarta da wani boka.

Kamar yadda ta bayyana, tun tana karama mahaifiyarta ta ke yi mata addu’ar kasancewa cikin farinciki da kwanciyar hankali.Budurwa ta faɗa tarkon soyayyar wani boka, ta wallafa bidiyonsu tare suna soyayya

Ta ce ta kusa karasa shekarar 2022 cike da cin zarafi da bakar azaba a Mexico amma sai ga shi ta hadu da masoyinta na kwarai, jaridar dimokuraɗiya na ruwaito.

A bidiyonta ba TikTok, ta wallafa shi ne wanda ta dauka tare da wani boka a bakin rafi wanda alamu ke nuna soyayya ce mai karfi ta kullu a a tsakaninsu.

Advertisment

Kamar yadda ta wallafa a tsokacin bidiyon:

“Dama wannan ne dalilin da yasa Afirka ke kirana tsawon shekaru? Tun ina karamar yarinya mahaifiyata ke min addu’ar zan zauna a kasata ta gado. Wajibi ne in kasance a nan don in yi ikirarin hakkin haihuwata, al’adata da kambuna! Ina son hakan.

“Duk da suka da azabar da na fuskanta a tsawon shekaru ashe akwai ranar da zan yi farinciki. Mamata tana yawan cewa halin da ki ke ciki zai wuce.”

Ya bayyana yadda ta azabtu a kasar Mexico amma sai ga shi ta samu masoyin gaskiya a kasarta ta gado.

https://www.tiktok.com/@vodounafricana/video/7181480509027978542?_r=1&_t=8YX9jupfmuE&is_from_webapp=v1&item_id=7181480509027978542

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button