Bidiyon Yadda wata matashiyar Mata take yiwa mijinta rawar Kwan kwaso yaja hankalin mutane
Wata mai amfani da shafin TikTok ta wallafa bidiyon dake nuna yadda yadda take takura wa abokin rayuwarta yayin da yake zaune dan shan iska.
Maya Kay ce ta wallafa ɗan takaitaccen bidiyon, wanda ya nuna tana rawar wakar Buga a kan cinyoyin mijinta, waƙar da ta haɗa Kiz Daniel da Tekno. Legit na ruwaito
Mutumin dai na zaune kuma ya maida hankali kan wani abu can daban amma matar ta matsa ya watsar da komai ya koma kanta yayin da ta zo sa salon rawa.
Matar ta taka rawar Buga a gaban mijinta
Abin sha’awar matashin magidancin ya ƙi nuna fushi wanda a cewar matar dan haka ta kirkiri rawar a gabansa.
Bidiyon ya ja hankali ma’abota amfani da dandalin sada zumunta watau TikTok, da yawa sun garzaya rashin faɗar ra’ayoyi sun tofa albarkacin bakinsu.
Kalli bidiyon da matar ta wallafa a nan
@maya_kay0 This is what you signed up for Oga????#maya_kay0#couplevideos#marriage#husbandwife#viralvideo#dance#fyp
Mutane sun maida martani
Queen Vashaty tace:
“Wa ya ga Felicia Osei a nan, gaskiya kun dace da juna.”
abenaconstance507 ya ce:
“Ta faɗa masa ya tashi tsaye amma har yanzun yana nan zaune abinsa.”
@Bless Kuzagbe558 ta ce:
“Haba ‘yar uwa kin matsa da yawa fa.”
@Joebel_Klodin ya ce:
“Kalle shi ya wani wayance kamar ba ya jin daɗin abinda take yi.”
Mutane sun maida martani Queen Vashaty tace: “Wa ya ga Felicia Osei a nan, gaskiya kun dace da juna.”
abenaconstance507 ya ce: “Ta faɗa masa ya tashi tsaye amma har yanzun yana nan zaune abinsa.” @Bless Kuzagbe558 ta ce: “Haba ‘yar uwa kin matsa da yawa fa.” @Joebel_Klodin ya ce: “Kalle shi ya wani wayance kamar ba ya jin daɗin abinda take yi.”