Bazan iya fitowa fim ba sai An biyani sama da Naira Miliyan Daya ₦1M – Hadiza Gabon
Sai An Cakemin Milliyan Daya Cass Kafin Na Yarda Na Sake Fitowa A Wani Sabon Fim, Idan Kudi Basu Kai Milliyan Daya Ba Bazan Sake Yin Wani Fim Ba, Cewar Jaruma Hadiza Gabon
Shahararriyar Jarumar Nan Hadiza Aliyu Wacce Akafi Sani Da Hadiza Gabon, Ta Bayyana Cewa Ita Daga Yanzun Idan Har Kudin Sallamarta Bai Kai Naira Na Gugan Naira Har Milliyan Daya Ba, To GasKiya Ita Bata Sake Fitowa Kuma A Wani Shiri.
Ta Bayyana Hakane A Sabon Shirinta Da Take Gabatarwa, Mai Suna “Hadiza Gabon Talk Show” Inda Take Tattaunawa Da Jarumai Da Dama.
Ta Kuma Shaidar Da Hakan Ne A Hirar Da Tayi Da Bakuwarta Fati Washa. Ga Abin Da Hadiza Gabon Din Take Cewa.
” Acting bai fita kai na ba, amma duk wanda ya sanni ko ya taɓa yin aiki dani yasan ina zaben script.
Idan an kawomin script zan karanta script idan scrip din yayi min zan sanni.
Zan iya tuna akwai wani wanda ya kawomin script bazan kira sunan sa ba, na karanta script naga na taba yin irin wannan Role din, bawai bana iya yin aikin ba a’a na taba yin wannan role din so sai nace amma bazan yi ba.”
Amma idan ankawomin script naga mai kyau ne zan iya yi idan yana da kudi masu yawa zan iya yi shine kawai.
A gaskiya bazan iya fitowa fim daga milliyan daya abinda yayi sama ba.”
Ga bidiyon nan zaku iya saurara kuji.