Bayan Korar Kare da Dan kishiya yayiwa mata shekaru 9 ɗiyarta ta Saye mata katafaren Gida Na ji da Fadi
Wata mata cike da hawaye farinciki ta bayyana yadda diyarta ta siya mata dankareren gida, dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
Diyarta ta bayyana cewa shekaru tara kenan da aka yi muku korar wulakanci daga gida gado kuma mahaifiyarsu ita ta cigaba da daukar nauyin kulawa dasu.
Bayan shekaru budurwar ta samu kudi kuma cike da sirri ta siya wa mahaifiyarsu gida mai kyau.
Bidiyon ya nuna yadda matar ba tare da saninta ba aka ja ta har gidan inda aka mika mata makullai.
Yadda tayi a bidiyon ya karya zuciyar mutane da dama. Yayin wallafa bidiyon a TikTok, @esther ta ce:
“Kun ga yadda na ba mahaifiyata mamaki ta hanyar siya mata gida. Na sanar da ita cewa na siya fili ne kuma yayana zai kai ta can don taga filin ba tare da ta san cewa kammalallen gida bane.
“Na ji dadin yadda na sanyata ciki farinciki. Kin cancanci fiye da haka mahaifiyata. Shekaru tara kenan da yayana wanda muke uba daya ya kore mu daga gidan gado.”
@___e.sther Dis was how I Suprise my mum???????????????????????????????????????????????????????? am glad I was able to put a smile on ur face mummy ???????????? u deserve more!!! 9 years ago my step elder brother chase us out of d house after d death of our dad, dad’s family never asked after us nor care for us! But u see God, he can never be a MAN!???????? #fyppppppppppppppppppppppp #fypシ #newhouse #family #viral ♬ Iyes’ogie – Princess Peters