Ba kora ta Ganduje yai ba, ‘wannan ƙarya ce mai gishiri’- in ji Baba Impossible
Tsohon Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Kano, Muhammad Tahar Adam, wanda aka fi sani da Baba Impossible, ya ce shi ya ajiye muƙamin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bashi a raɗin kan sa.
Da ya ke magana a Freedom Radio a yau Asabar, Baba Impossible ya bayyana cewa tun a jiya Juma’a ya rubuta takardar ajiye aiki ya kuma kai wa Sakataren Gwamnati, Alhaji Usman Alhaji da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamna, Usman Bala, kwafin na gwamna kuma su ka buga masa stamfi. Daily Nigerian Hausa na ruwaito.
A cewar Baba Impossible, bayan ya kai takardar, abin mamaki kawai sai ya ga an fitar da sanarwa cewa wai Gwamna ya kore shi sabo da ya na aikata abubuwa marasa kyau kuma ba ya biyayya ga Gwamna.
“Wannan abin mamaki ne sabo da ni a gani na, cikakkiyar gwamnati ba za ta yi karya ba. Wannan ƙarya ce mai gishiri.
“Bayan na riga na kai takardun murabus di na kuma an karɓa sannan kuma wani ya fito ya ce wai an kore ni.
“To wannan magana an rufe ta kuma mun bari, amma idan sun ci gaba za ku ci gaba,” in ji Baba Impossible.