Labarai

Argentina na shawarar sanya hoton Messi a jikin kuɗi B

Babban Bankin Argentina na shawarar sanya hoton gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya a 2022, Lionel Messi a kan takardar kudin ƙasar na peso 1,000.

Argentina na shawarar sanya hoton Messi a jikin kuɗi
Argentina na shawarar sanya hoton Messi a jikin kuɗi

A cewar Daily Mail jiya Alhamis, jaridar Argentina, El Financiero, ta bayyana cewa babban bankin ƙasar Argentina na son ya kafa wani abu na tunawa da nasarar da tawogar ƙwallon ƙafar ƙasar ta samu a Qatar, mai cike da tarihi kuma tun kafin wasan da ta samu nasara kan Faransa a ranar Lahadi ba kin ke tunanin kan hakan.

A wani cikakken bayani da jaridar ta EF ta wallafa, cewa muhimmin bangare na dalilin da ya sa a ke tunanin sanya hoton Messi a jikin kuɗin peso 1,000 shi ne cewa lambar rigarsa ta Argentina lamba 10 ce.

A tsarin kuɗin, za a saka fuskar Messi a gefe ɗaya, inda gefe ɗaya kuma za a rubuta sunan tawogar ƙasar ‘La Scaloneta’ shine da aka tsara a bayan takardar kuɗin.

Kalmar ta zama daidai da wannan rukunin tun lokacin da Lionel Scaloni ya gaji Jorge Sampaoli a 2018.

Messi ya jagoranci Argentina ta doke Faransa a gasar cin kofin duniya ta 2022 a karon farko tun 1986.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button