Labarin yarinya ita da iyayenta sunka zo Nigeria daga kasar faransa domin haddata ce alkur’ani mai girma cikin wata shidda ta tabbata gaskiya inda a yau ne anka baiwa hafiza fatima musa kyauta wadda mai martaba sarkin musulmi Sultan sa’ad Abubakar Muhammad Na III.
Inda jaridar bbchausa ta ruwaito yadda anka yi bikin bada kyauta.
“Wata yarinya ƴar ƙasar Faransa ta haddace Al-Ƙur’ani mai girma a cikin watanni huɗu a birnin Zaria na Jihar Kaduna.
Yarinyar mai suna Fatima Musa wadda iyayenta suka koma Najeriya daga Faransa ta soma haddar ne a wata makaranatar Islamiyya a Zaria inda ta rinƙa haddace shafi takwas na Al-Ƙur’ani a duk rana.
A yau ne aka yi bikin saukar haddar inda ɗaya daga cikin manyan baƙin da suka halarci saukar har da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III da Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sarkin Kazaure Najib Hussaini Adamu da sauran manyan sarakuna.
Hukumar makarantar ta ce wannan ne karo na farko da ta samu ɗaliba mai irin wannan hazaƙar.”
Zaku iya kallon bidiyo kira’ar hafiza Fatima Musa a Nan