Kannywood

An Baiwa Jarumin Shirin Film Ɗín Labarina Shiri Maì Dogon Zango Sarauta A Gombe

Shiri mai dogon zango wanda kamfanin Saira movies yake a halin yanzu wanda ana cikin zango na shidda inda yau ne za’a fara nuna Kashi na daya wato Episode 1 a turance wannan fim ya anya an baiwa wani jarumi sarauta kamar yadda Shafin Dokin Karfe tv a shafinsu facebook sunka wallafa.

Sarkin masarautar Kalshingi dake jahar Gombe, Alhaji Hussain Abubakar Magaji ya bawa jarumin Shirin film din Labarina mai nisan zango a karkashin masana’atar Kannywood, Áliyu Ibrahim(Haidar) Sarautar DAN ADALAN KALSHINGI..

An Baiwa Jarumin Shirin Film Ɗín Labarina Shiri Maì Dogon Zango Sarauta A Gombe
An Baiwa Jarumin Shirin Film Ɗín Labarina Shiri Maì Dogon Zango Sarauta A Gombe

Dalilin bashi wannan sarauta shine ganin kokari da gudunmawa da yake bayarwa cikin shirin da sauran fina-finai da kuma wakoki da yakeyi cikin harshen Hausa, wanda hakan yana taimaka wajen bunkasa harshe da al’adun Hausa.

A kokarin masarautar na wanzar da alaka tsakanin Aliyu Ibrahim Haidar da masarautar yasa taga cancantar bashi wannan sarauta ta DAN ADALAN Kalshingi.

Wanda wannan sarauta ta DAN ADALAN KALSHINGI shine mutum na farko da ya fara rikewa ta, masarautar ta nuna farin ciki matuka da bashi wannan sarauta, kuma ta bashi kwarin sosai, kuma mai martaba sarkin yace Aliyu ya kara zage damtse wajen gudanar aikin sa na Film da wakoki, don bunƙasa harshen Hausa.

Da muka ji ta bakin jarumin wato Aliyu Ibrahim yace “Ina godiya da wannan sarauta da aka bani,Wanda zan Iya cewa cancanta ta jawo aka bani a matsayina na yaron jarumi kuma mawaki.,Wanda sarki ya kalli abubuwan da make bada gudunmawa yasa yaga dacewar cancantar bani wannan sarauta,to ina godiya da wannan sarki mai girma da daraja”

Áliyu Haidar ya bayyana godiyar sa ga sarkin Kalshingi bisa wannan girmamawa da karramawa da yayi masa ta bashi sarauta,kamar yadda Aliyu ya bayyana da bakinsa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button