Aminu Ala Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Bai Taɓa Yi Wa Sarki Sanusi Lamiɗo Waƙa Ba Lokacin Ya Na Sarkin Kano
A wani ɓangare na hirar mu da Alan, ya bayyana cewa: “Har abada Sanusi Lamiɗo Sanusi sunan shi Sarki duk da ba ya kan gadon sarauta”.
A cewar mawakin lokacin da hadiza Gabon take masa tambaya nan take yace
” Ke kinka fada? Tace a’a jijita taji a gari.
“Sai yace ae daman mutane ba’a rabasu da jita jita amma sarki Sanusi nama taɓa yimasa waka a lokacin yana dan majen kano.
Dan majen kano na kanawa shine taken wakar.”
“A Duniya dai tasan nida ado Bayero a lokacin ban taba haduwa da sarki sanusi ba, kuma bamu saba ba gaskiya ban ma taba ganinsa ba.
Saboda ni a lokacin da na taba ganinsa sai lokacin da ake wani taro mai suna “kano da masu ita” inda ankayi gayya daga baya irinsu bashir tofa su dantata da dangote da kowa har da BUA sai a lokacin naje na gaishe shi munka gaisa saboda bamu saba ba.
Wanda nafi sabawa da shi cikin ‘yayan sarki Ado Bayero shine Sarki Aminu Ado Bayero saboda duniya ta shaida haka duk inda zamuyi taro tare da shi muke.”
Ya kara da cewa babu wanda yace zo kayiwa sarki sanusi waka.”
Aminu Alan waka yace akwai rukunai ukku wanda sune yake yiwa waka kuma idan sarki sanusi ya shiga daga ciki zaiyi masa waka.
Ga cikakken rahoton wadda ke ƙunshe da bidiyon jawabin Alan Waƙan wadda za ku iya kallo ta na