2023 : Ba Za Mu Faɗa Wa Mutane Wanda Za Su Zaɓa Ba— Dr. Sani umar R/Lemo
Fitaccen malamin addinin Musluncin nan ɗan jihar Kano, Dakta Muhammad Sani Rijiyar Lemo, ya ce babu ruwan malamai da ‘yan takarar da ‘yan ƙasa za su zaɓa a matsayin shugabanni a zaɓen 2023.
Daktan ya bayyana haka ne a cikin wani gajeren bidiyo na karatunsa da Labarai24 ta ci karo da shi.
“Kai yanzu kai ne abin tambaya. Da can an danganta abin ga malamai, ga waye, ga waye, su za su zaɓa. To yanzu an ce kai ne za ka zaɓa. Saboda haka malamai ba ruwanmu.
“Ka je, duk abin da ka zaɓo. To an ƙwace daga hannun malamai. Saboda haka mu dai sai dai mu gaya maka abin da ya kamata ka yi. Kai kuma: “Mutum mai hankali ne akan kansa”.
“Ɗan’adam Allah ya ba shi basira, ya ba shi hankali. Saboda haka kai ka je, duk abin da ka yi, kai Allah zai tambaya”, in ji shi.
“Yanzu a zo a ce maka, wane, wane, wane, wane, kuma abu ya zo ya faru, ka je gaban Allah ka ce ce ai wane ne, malam wane ne ya sa ni. To ba ruwana.
“Ni dai na gaya maka. Basirar da Allah ya ba ka, idan kowa a buɗe yake, kuma zaɓen nan duk don duniya ake yin shi.
“Ba wanda za ka zaɓa don ya yi maka fatawa, ko ya gaya maka yadda ake salla, ko azumi ko zakka, bare a ce malam kai ka san wa yake da ilimi”, Dakta Sani ya ƙara da haka.
“Wannan abu ne na duniya. Ka samu abinci, ka samu abin sha, ka samu zaman lafiya, ka samu kaza, ka samu kaza.
“To kowa ya san waɗannan abubuwan. Kowa yana nema. Saboda haka ba sai an zo an ce maka wane da wane su za ka zaɓa ba. Don haka ya rage ga naka ka je ka zaɓa. Kuma can ku haɗu da Allah, kai ka san me za ka faɗa masa” a kalaman Shehin Malamin.