ƘARFIN HALI: Ɗan haya ya kai karar mai gida sabo da ta ƙi sayar masa da gida da ya ke ciki
Wata babbar kotu a Legas ta yi watsi da ƙarar da wani ɗan haya mai suna Ademola Onitiju ya shigar a kan mai gidan da ta bashi haya sabo da ta ƙi sayar masa da shi (gidan).


A shekarar 2021, Onitiju, wanda sojan sama ne mai ritaya kuma ma’aikacin shari’a, ya kai Theodosia Ogunnaike kotu a kan ta ƙi sayar masa da gida mai dakuna hudu a Dolphin Estate a Ikoyi, amma ta sayar wa da wani gidan bayan da shi ɗan hayar nata ta fara yin ciniki.
Ɗan hayar, mai shekaru 59, wanda ya fara zama a gidan a watan Disambar 2015, ya ce tun da fari, mai gidan ta yi masa tayin ya siya, amma kuma bai biya kuɗin ba bayan ya amsa cewa ya yarda zai saya.
Onitiju ya ce da farko an nemi ya biya Naira miliyan 170 kuɗin gidan amma sai ya biya Naira miliyan 90 a maimakon haka, sai mai gidan ta ƙi amince wa.
Ya ƙara da cewa, a lokacin da ake tattauna wa, ya sayar da kadarori biyu na gadon su domin ya samu damar sayan gidan a farashin Naira miliyan 135 wanda ya ce shi a haka zai saya.
Ya ce ya nemi matar da bashi lambar asusun bankinta domin ya biya kudin ta nan, amma ba ta ba shi komai ba har sai da aka sayar da gidan ga wani Samuel Dare, wani Kanar ɗin soja mai ritaya.
Ogunnaike, wacce bazawara ce ta ce gidan na ƴarta ne amma ita ke kular mata da shi.
Matar ta ce Onitiju ya kasance ya na biyan kudin hayar sa na Naira miliyan 4.5 a asusun ajiyarta na banki duk shekara kuma ba a kara kudin hayar ba a lokacin zamansa sabo da su na zaune lafiya.
Uwargidan ta ce an fara ba Onitiju tayin sayen gidan, amma ba shi da kudin da zai biya. Daga nan sai ta dakatar da tayin da aka yiwa jami’in sojan sama mai ritaya bayan yayi tayin kudi guda biyu na naira miliyan 90 da kuma naira miliyan 100, inda da ga nan ne ta buɗe kofar sayar da gidan ga kowa da kowa.
A hukuncin da ta yanke Bola Okikiolu-Ighile, shugabar alkalan kotun, ta ce shaidun Onitiju da ke gaban kotu ba su da wani karfi da za su kare ƙorafin da ya shigar ba kuma bashi da gaskiya a shari’ar.
Daga baya ta yi watsi da karar.