Yadda Dan Shekaru 32 Ya Auri Mata 3 Lokaci Daya, Uwa Daya
Wani mutum mai suna Luwizo ya gwangwanje ta hanyar auren mata 3 rigis lokaci daya.
Mutumin mai shekaru 32 da yake bayyana yadda lamarin ya faru ya ce, ya hadu da Natalie wato daya daga cikin yan uku a facebook, kuma da tafiya tayi tafiya sai suka fara soyayya.dimokuradiya na rahoto
Bayan soyayya tayi nisa ne kuma sai suka yanke shawarar haduwa da juna domin gaisawa, wanda kuma suka shirya haduwa a tsakanin su.
Ya ce bayan ta gabatar da shi a gaban yan’uwanta mata biyun, sai suma suka kamu da son sa, wato Natasha Da Nadege.
Wizo ya ce yayi matukar mamaki lokacin da ya tambayi iyayen ta cewa yana son auren ta, domin kuwa sun tabbatar da cewa sai dai ya dauke su baki daya domin yan uku ne.
A cewar mahaifan ta tunda dai sun kasance yan uku don haka baza a raba su ba dole ne su auri mutum ɗaya, wanda kuma zai basu kulawar da ta kamata.
Da aka tambaye shi ko yaya zai iya hada su waje daya tare da kula da su, daya daga cikin matan ta ce dolen sa ya hakura ya aure su saboda ya riga ya kamu da son daya daga cikinsu.
Ko da Lawizo ta sanar da iyayensa abunda ke faruwa sun gaya kin amincewa da fari, wanda hakan ya sa suka kauracewa zuwa bikin nasa, amma shi kuwa Ya ce baya nadamar hakan.
Matan uku dai sun kasance uwar su daya.