Yadda Ake Hira Da Mace /Budurwa Sabuwar Kamu
Malam Ina gaisuwa.Tsakani da Allah Ina son yarinyar nan amma ban san yadda zan fara tattaunawa da ita ba. Da fatan za a taimaka.
Malam Tonga ina gaisuwa. Akwai Wata dana soma soyayya da ita, wannan yarinyar ban san me zan rubuta ba. Kuma gashi ba na son rasa ta. Wadanne irin hira da tambayoyi zan yi mata idan muna hira?
Da fatan Malam Ya wuni lafiya.
Malam ina son wata budurwa ce ‘yar Jami’ar danake karatu amma wallahi na rasa yadda zan tinkareta da zancen soyayya.
Don Allah Malam ataimaka.
Wadannan wasu sakonni ne danake samu daga wajen samarin da suke son sanin irin hiran da zasu rika yiwa ‘yan matan su sabbin kamu. Wasu kuma suna son sanin dabarun da zasu tinkari macen da suke so a karon farko.
Mun sha yin darusa akan dabarun tinkaran mace. Sai dai irin hiran da namiji ya kamata yayi da sabuwar kamunsa shine bamuyi su da yawa ba. Kuma tun a tsohon shafin Tsangayar mu muka yi. Wannan yasa zamu yi bayani ne akan sa.
Ba wai kawai samun soyayyar mace shine abun bukata ba. Rashin sanin yadda zaka yi hira da mace na iya sa ka rasa wannan budurwa da ta amince da soyayar ka.
A dabi’a ta mace, tana son namiji shuru shuru. Amma bata son namiji mara magana. Shi shuru shuru saboda son kanta na kada ya saba da wasu matan da kuma zai yi sauki kai da kowace mace ma zata nemi yin kusa da shi. Wannan yasa mata suke sons maza masu shuru shuru. Amma sam bata kuma son saurayinta ko mijinta yaza mutumin da bai magana gum, ko bai iya hira ba. Saboda mace duk yawan maganarta da surutunfa tana son taji wanda take so shima yana cewa.
Wannan rashin iya hira da mata yasa samari ko nace maza da dama suna ji suna gani suka rasa soyayyar su wajen matan da suke so.
Sai dai abu na farko da namiji zai soma la’akari dashi shine, hira ya zame masa dole koda kuwa ba dabi’ar sa bane domin tabbatar da ya samu abunda yake nema. Don haka dole ne ya daure ya koyi sakin baki a gaban wacce yake so domin gudun kada wani mai iya zance yayi wuf da ita.
Zance da mace musamman sabuwar kamu yanada matakai. Saboda a wannan lokacin baku gama sanin juna a soyayance ba koda kuwa a gida guda kuka taso. Don haka akwai maganganu ko tambayoyin da bazaka mata ba a farko farkon soma soyayyar ku.
Mu dauka ka riga da ka samu soyayyar ta zaka soma zuwa wajenta hira, tadi ko zance. Akawai wasu matakan hira guda 7 da su ya kamata duk wani sabon masoyi ya yiwa sabuwar kamunsa. Wadannan matakan kuwa sune kamar haka:
1: Tamboyin neman saninta da kyau: Wannan shine hiran da duk wani sabon sauryi zai soma yiwa sabuwar kamunsa.
A wannan lokacin akwai wasu abubuwan da zaka so sani game da ita masu mahimmanci. Kamin ka bata dama ita ma ta yi maka nata tambayoyin.
A wannan lokacin kai aikinka sauraro ne wajen bata hankalinka, da kuma mata karin tambaya akan bayanin da baka gane ba ko baka fahimceta ba.
A wannan yanayin itace zata zama mai maganar ba kai ba. Amma domin hira ya mata dadi, kuma taji cewa hira take da masoyinta, dole ne ka tabbatar baka amsa wayarka ba ko wasa da wayar taka ba. Haka kuma ya dace ka rika binta da tabbatar mata kana sauraronta yadda ya dace da kuma fahimtarta ta hanyar amsa mata da kuma kada kanka amatsayin kana gamsuwa da jawabin nata.
Awannan lokacin ka tabbatar da cewa idanuwanka yana kan fuskanta kana mata kallon soyayya da kauna. Kada ka maida hankalinka wajen kallon kirjinta idan mai yalwar kirji ce. Hakan zai sa ta maka fassara na daban. Amma kallon fuskanta da kwayar idanuwanta aikawa ne da sakon soyayar ka gareta. Rashin kura mata idanuwa kuma zai nuna tamkar bata maka bane. Don haka ajiye kunya zaka yi a gefe kayi abunda ya dace.
A wannan lokacin da take magana idan baka fahimci wani waje ba ko bakaji sosai ba, yi mata magana cikin wayewa na baka fahimceta ba. Kada ka barta tayi ta zuba kamar tana hira da Dan jarida ne ba tare da kana katsaita kana mata wasu tambayoyin ba. Hakan yana nuna mata kana tare da ita kuma kana gamsuwa da amsar da take baka.
Kamin ka san irin tambayoyin dasuka dace da zaka yiwa sabuwar kamunka, yana da kyau ka fahimci cewa, shi sabon masoyi duk yadda yake son hira da sabuwar kamunsa ba a so ya jima. Don haka kada ka sake idan kaje sai an turo ta shiga gida ko kuma lokacin shiganta gida yayi kana tare da ita.
Dogon lokaci kana hira da ita zai jawo kayi ta maimaita batu iri guda, ko ka rasa ma abun cewa idan ba hadawa zaka yi da karya ba kuma abunda ba a so kenan.
Hakan nan jimawa da ita ba zai baka damar ta zama tana dokinka ba. Zaka yi ta zuba ne ko ka yi ta sata surutu har sai ta gaji da kai. Don haka ne ba a son jimawan a lokacin da kuke tsakiya da hira zakayi sallama da ita.
Haka nan takaita doguwar hira wajen sabuwar kamunka nasa iyayenta idan masu hankali ne su fahimci kanada tsari. Kanada abunyi ba mara aikinyi bane koda kuwa shidin ne.
Rashin barin har sai mace tace maka zata shiga gida ka sallami kanka yana cusawa mace shakku a ranta da zata rika jin abun na damunta a rai. Zata rika tunanin kodai itace bata yin abunda zai saka jimawa a wajenta, ko kuma kana barinta kaje wajen wata budurwa wace. Wannan wannan shakkun ribace a soyayyar ka.
A darasi na gaba zamu kawo irin tambayoyin da suka dace kayiwa mace sabuwar kamunka a sabon soyayyar ka da ita.
~tsangayamalamtonga