Labarai

Ya Saki Amaryarsa A Daren Cin Amarci

Wani ango da aka daura aurensa a wannan makon ya saki matar tasa a daren da suka fita cin amarci.
Lamarin ya faru ne inji mai bamu labarin bayan da ango ya dauki matarsa zuwa wani otel na cikin garin domin su kauracewa hayaniyar ‘yan buki su kuma samu damar cin amarci. Don haka ne ya tafi daya daga cikin manyan otel na garin domin ya samu dakin da zasu kwana.

Ya Saki Amaryarsa A Daren Cin Amarci
Ya Saki Amaryarsa A Daren Cin Amarci

Sai dai abun mamaki duk dakin da aka ambata a hotel din duk da yawan dakunan sai ta fadi aibun dakin.

“Ina daya daga cikin abokan angon shi yasa ma na kiraka na baka labarin abunda ya faru. Tare da shi muka je otel din nan. Abun mamaki Malam Tonga duk lambar dakin da aka ambata sai tace bai yi mata ba, Inda aka tambayeta dalili sai ta fadin illar dakin. A haka sai da muka sauya dakuna 7. Daga karshe ita da kanta ta fadamana lambar dakunan hotel din masu kyau tace idan akwai su babu kowa a ciki a bamu. Kuma yadda ta fadi matsalolin dakunan haka nan masu nuna dakunan suke tabbatarwa. Hatta dakin da muka kama sai da ta fadi matsalar AC da talabijin na dakin da yadda gadon yake hade da bangon dakin kuma haka abun yake kamar yadda ta fada.

“Wannan abun ya matukar daga mini hankali amma sai na daure saboda bana so abokina ya gane. Bayan mun shiga dinkin ne na rako su zan fita sai ya dakatar dani. Yace na samu waje na zauna. A zato na magana zai mini akan hidimar bukin, sai naji yana tambayar amaryarsa yadda aka yi tasan matsalolin dakunan otel din, daga nan ne fa ta soma rantsai rantsai akan ita an fadamata tun Kamin muzo otel din ne. Kawai sai naji yace mata wacce na sake ki saki daya”. Inji abokin ango.

Sai dai ganin yadda al’amarin ya kicibe inji mai bamu labarin, nan take ya kira sauran abokan sa aka taru domin sasanta lamarin, inda da kyar angon ya amince ya dawo da ita bayan nuna masa kila ba yadda ya dauki abun haka abun yake ba.

Idan kaine zaka dawo da ita ko dai kayi sakin kenan?

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button