Wasu Alfanun Da Duk Namiji Zai Samu Guda 5 Idan Yayi Aure Da Wuri
1: Zai Samu Lokacin Yiwa Abunda Ya Haifa Tarbiya
2:Zai Gwangwaje Soyayya Da Matarsa Ko Matansa
3:Zaka Samu Shakuwa Da Abunda Ka Haifa
4: Zaka Samu Damar Zama Shugaba A Gidanka
5: Zaka Samu Hutu Tun Da Sauran Karfinka
Yadda Zaka zama Uba Na Gari
Ba yin aure ko dace da haihuwa bane abun ji ga duk wani magidanci ba, amma yadda zaka kula da abunda ka haifa shine abun ji.
Allah ne Yayi umurni da yin aure, sai dai babu ruwan Allah ga duk bawanSa daya kama gareshi bai yi aure ba. Sai dai kuma duk wanda yayi aure harma ya haihu, a nan ne Allah zai nemi sanin yadda ya kula da iyalansa. Wanne ne ma yace magidanta maza suyi duk mai yiwuwa domin ganin sun kare Iyalansu daga shiga hutar jahannama.
Ga wasu matakan da zaka iya binsu domin zama uba na gari.
1:Ka tabbatar da cewa a matsayinka na Uba na gari, ka kula da dukkanin hakkolin ‘ya’yanka.
Karatunsu, sutura da abincinsu da taya matarka yi musu tarbiya suna daga cikin hakkolin duk wani Uba na gari.
Haka nan kaine zaka kare musu duk wani hakkinsu ka kuma horas dasu jarumta, tausayi da taimako.
2: Duk wani Uba na gari ya zamanto yana da dabi’u da halaye masu kyau da abunda ya haifa zasu iya koyi dashi.
Shan taba sigari, yawan furta kalamai ko zagi na rashin daraja duk ba abun da Uba na gari ya dace yayi a gaban yaransa bane.
Uba na kwarai bazai taba yin wani abun da zai koyar da yaransa mara kyau ba. Kama daga furuci ko a aikace.
3: Idan kana so ka zama Uba na gari dole ne sai kana samun lokaci da yaranka kana shiga cikinsu kana maida kanka yaro kaima da sakin jiki dasu domin fahimtarsu.
Shiga ko jawo yaranka kusa dakai suke jawo shakuwa da kauna a tsakanin Uba da yaransa.
4:Uba na gari yakan mutunta yaransa tare da girmamasu da saurarensu. Idan ka musu laifi ko kuskure ka basu hakuri. Idan sun maka abun kirki ka gode musu da musu insani. Idan sun Maka kuskure ka musu gyara ta hanyar nasiha.
5: Uba na gari yana karfafawa yaransa gwaiwa wajen wani abu da suka zo da shi mai kyau. Yakan kuma tallafa musu domin ganin sun cimma burinsu na rayuwa.
Kada ka soma idan kasan bazaka zama Uba na gari ba. Allah Ya Talllafa Mana A Kokarin Mu na zama iyaye na gari