Uwar Budurwata ta Rokeni da nayiwa ƴarta ciki – cewar saurayi
Mahaifiyar budurwata ce ta nemi na yi wa ‘yarta ciki- Matashi
Matashin da ake zargin ya dirka wa budurwarsa ciki a jihar Oyo ya sanar da kotun da ke yi masu Shari’a a birnin Ibadan babban birnin jihar cewa mahaifiyar yarinyar ce ta roki ya yi wa ’yarta ciki kafin su yi aure.
Budurwa ce dai ta kai karar wannan matashi kotu don a raba tsakaninsu inda ta ce bayan ya yi mata ciki ya daina kula da ita da abin da ta haifa masa yadda ya kamata.
Matashin ya fada wa kotu cewa iyayen budurwar ne suka nuna cewa yar tasu ba za ta zauna da shi ba kuma a karshe aka rika hana shi ganin abin da budurwarsa ta haifa.
Karanta wani labari Na Kama Mijina Da Mahaifiyata Turmi Da Taɓarya Suna Jima’i – inji wata mata
Na Kama Mijina Da Mahaifiyata Turmi Da Taɓarya Suna Jima’i, Wanne Mataki Ku Ka Ga Ya Dace In Ɗauka? Cewar Wata Matar Aure
Wata matar aure da ke zama a jihar Gombe amma mijinta yana aiki a Abuja ta bayyana yadda da tsakar dare ta kama mijinta da mahaifiyarta su na lalata, kuma har ta gansu ta bar wurin ba su kula da ita ba
“Tun da nake zaune da mijina, bai taɓa ɓata min rai ba ko kuma yayi min wani abu na musgunawa, amma a wannan karon kaina ya kulle sakamakon abinda na gane wa idanu na.”
Mahaifina ya rasu, hakan yasa bni da wacce ta wuce min mahaifiyata. Bayan na haihu ne mahaifiyar tawa ta je gidana da ke Gombe don tayi makonni uku na zaman jego.”
“Dama kullum sai mijina ya bani fura, ashe yana sanya min maganin bacci a ciki, amma ranar da dubunsu za ta cika ban sha furar ba.
“Farkawata ke da wuya, sai ban ga mijina a gefe na ba, hakan yasa na yi tunanin ko ya shiga ban ɗaki ne, kasancewar ɗakuna biyu na kwana gare mu, sai na yanke shawarar komawa ɗaya ɗakin don na yi amfani da bayin.”
Shiga ta ke da wuya na ga mijinta da mahaifiyarta su na lalata, sai Ubangiji ya sanya man nutsuwa na lallaɓa na koma ɗaki na kwanta cike da damuwa.”
“Hakan yasa nake neman shawarar yadda zan ɓullo wa lamarin.” In ji ta