Tsugune Bata kare Ba – Kotu ce zata Rabamu Da Ali Artwork – Sarkin waka
Sarkin Waka Ya bayyana cewa Kotu ce Zata rabasu da Ali Artwork Akan Tsarginsa da yayi na cewa Ya Cinye Miliyan 25 aci kuma harda Kudinshi inda ya bashi Naira 50,000 Kawai.
Kamar yadda Aka sani an Samu rikici Tsakanin Mawaki Naziru Sarkin Waka tare da Ali Artwork wanda akafi sani da madagwal Inda Ali Artwork Ya dora Zargi akan Sarkin waka cewa ya cuceshi akan kudin kampen da aka bada na tafiyar Wazirin Adamawa alhaji Atiku Abubakar.
Asalin dai rigimar ta fara ne Tsakanin Fitaccen me wasan barkwanci nan me suna Mazaje tare da Ali artwork, inda shi mazajen ya bayyana cewa Sunje Wajen Mataimakin gwamnan jahar kano Alhaji nasiru Yusuf gawuna wanda a karshe ya basu kudi Naira Miliyan daya amma sai Ali artwork ya cinye kudin ya hanashi.
Ga sautin muryar sarkin waka nan ku saurara.
A cikin wannan sautin murya sarkin waka yace yana tunanin bazai kyale shi ba domin banaso na yarda da kai na turamaka abu ba, kai kuma ka daukota ka fita da ita waje ba.
Sarkin waka ya kara da cewa da ka cimin amana gara ka zageni.