Shin Da Gaske Ne Dr. Idris Abdul’aziz Bauchi yaci Mutuncin Prof.Isa Ali Pantami?
A safiyar yau an waji gari da wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda majiyarmu ta samu wannan ya fara fitar da wannan bayyani shine wani almajiri mai suna Abdullahi Sautussunnah Biu ya wallafa a shafinsa na sada zumunta wanda kowa yake ta wallafa ga abinda ya wallafa a Shsfinsa.
“DR. IDRIS ABDUL’AZIZ BAUCHI YA CI MUTUNCIN PROF. ISA ALI PANTAMI AKAN MINBARIN JUMMA’A!
Akwai abun mamaki sosai yadda Dr. Idris Abdul’aziz Bauchi ya ci mutuncin Professor Isa Ali Pantami cikin rashin adalci da son kai akan minbarin jumma’a ya aibantasa ya siffantasa da duk irin siffarda ya gadama tabbas Dr. Idris ya bamu kunya a matsayinsa dake kiran kansa Ahalussunnah
KAƊAN DAGA CIKI:
1- Ya kira Prof. Isa Ali Pantami da makaryaci karara yace “makaryaci”
2- Ya kira Prof Isa Ali Pantami da cewa bashi da alaka da Addini harma cewa ya yi masu faɗin cewa Prof. Isa Ali Pantami yanada alaka da addini wai masu faɗin haka basu san addini bane!
3- Kuma sannan ya kira Pantami da cewa babu wani ci gaba na addini da ya kawo da hawansa minister
4- Hakanan ya nuna cewa duk tsare-tsarenda Pantami ya yi wahalar da mutane kawai ya yi musamman akan wannan harkar NIN
5- Yace tunda Prof Pantami yaje wannan matsayi babu abunda ya tsinanawa musulunci in banda neman kuɗinsa da yake yi
Wallahil azim wannan babban abun kunyane ga wannan Dr. Wato Dr. Idris Abdul’aziz idan ba abun kunya za’a kira ba me za’a kira wannan batun?
Ya fito ya bayyana hassadarsa karara akan Prof. Isa Ali Pantami ba tareda ya ji kunya ba, Tareda cewa kuma wannan abun kunya yayi ba babban abun kunyarma shine dukkan abubuwanda ya faɗa akan Prof Isa Ali Pantami duk karya ne
Yanzu dan Allah me yake son nunawa al’umma cikin waɗannan maganganun nasa?
So yake mu zagi Prof. Pantami kamar yadda ya ci masa mutunci ko kuwa so yace mu daina kallon Prof. Pantami da daraja??
Allah rabamu da malaman zamani ƴan neman tada hayaniya da fitina cikin al’umma
Ameeen”
To sai dai hausaloaded tayi kokari ta samu bidiyon da malam Dr. Idris Abdul’aziz Bauchi yake maganar daga bakinsa ga bidiyon nan ku saurara kuni gaskiyar abinda ke faruwa.