Labarai

(Bidiyo) Sanadiyar Kisan Daliɓi Khalifa Wanda Abokan Karatun Shi Suka Kashe A Makarantar Lafiya A Jihar Sakkwato

Labari ne mai sosa rai da tausayi da takaici haɗi da tsotsayi acikin wannan lamarin da yafaru ga ‘yan makarantar gwadabawa. Majiyarmu ta samu wani matashi  Real Buroshi Mawaka Sokoto  ya tattara wannan labarin inda jiya munka kawo labarin amma banda asalin abinda yasanya hakan.

Matashin ɗalibin maisuna Lukman wanda akafi sani da Khalifa ɗan garin kalambaina mai karatun sashen lafiyar haƙori ( Dental&surgery) a makarantar lafiya dake gwadabawa ta jihar sokoto, ya haɗu da ajalinsa ne ta sandiyar bugun taron dangin da wasu ɗalibai haɗi da abokinsa kuma amininsa suka mishi ta hanyar ɗaure shi da igiya suna azabartar dashi wanda hakan yayi sandiyar mutuwarsa har lahira akan zargin da sukayi mishi na satar waya.

Labarin da nasamu daga hukumar makarantar ya tabbatar min da gaskiyar abunda yafaru cewa ” Ɗaliban sunje sun tayarda margayin ne da misalin ƙarfe 2 na daren Lahadi 20-11-2022, inda suka fara sa’insa a tsakaninsu akan tuhumar da suke mishi na satar waya, daganan ne suke tilasta margayin da sai ya amsa zargin da ake mishi na dole sai ya basu wayarda suke tuhumar ya ɗauka” Bayan hakan bata samu ba sai suka rinjaye ƙarfin khalifa har yakai suka ɗaure shi suna mishi bugun akawo Wuƙa acikin daren tareda watsa mishi ruwan sanyi a wannan yanayin, tun daganan ne rai yayi halinsa kamar yanda wani shaidar faifan bidiyo ya bayyana inda ake jin muryoyinsu da irin kallon azabar da suke yiwa margayin.

 

A halin yanzu ankama mutun biyar Waɗanda ake zargi da ballewar mutun ɗaya ɗan asalin jihar kaduna wanda aka tabbatar cewa ya gudu ana tsakar bincike a asibitin Uduth dake nan cikin ƙwaryar birnin Sakkwato, wanda daga bisani aka kama direban da ake tuhumar ya boye yaron da ya gudu har sai ya fa fito da yaron a inda yake kafin asake shi.Sanadiyar Kisan Daliɓi Khalifa Wanda Abokan Karatun Shi Suka Kashe A Makarantar Lafiya A Jihar Sakkwato

Mahaifiyar margayin ta tabbatar da jadadda yafiyarta ga Waɗanda suka yiwa khalifa kisan gilla, saidai hukumar makarantar tace ” Sam bazasu yafe ba har sai sun ɗauke mataki ga Waɗanda suka kashe ɗalibin nasu maisuna khalifa domin hakan yazamo izna da darasi ga sauran mutane” sun ƙara da cewa ” idan har ba’a ɗauki wannan matakin ba watarana hakan zata iya sake faruwa ga wasu ɗalibai wanda ba’a fatar sake faruwar hakan.

A yanzu dai yaran da ake zargi da kisan margayin, tuni an kama su kuma suna a hannun hukumar bincike ta C.I.D dake birnin Sakkwato, inda daganan ne zan cigaba da bincike akan matakin da hukumomi zasu ɗauka akan wannan lamarin.

ALLAH Ya Jikansa Da Rahamarsa Yakara Karemu Daga Miyagun Qaddarori Yasa Ayi Shari’a Daidai Da Gaskiyar Abunda Aka Tabbatar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button