Rarara ya bayyana Alakarsa Da Aisha Humaira
Mawaki Dauda Rarara Kahutu, Ya Bayyana Alaqar Dake Tsakaninsa Da Jaruma Aisha Humaira, Mawakin Ya Bayyana Hakan Ne A Hirar Da Sukayi Da Jaruma Hadiza Gabon, Inda A Shirin Nata Take Zantawa Da Jarumai Da Kuma Mawaka. Shafin hausamini ya rahoto
Aisha Humaira Dai Tana Daya Daga Cikin Jarumai Mata Da Tauraruwarsu Ke Haskawa A Masana’antar KannyWood, Sai Dai Anga Lokaci Guda Ta Jingine Harkar Fina Finan Ta Koma Karkashin Kamfanin Mawakin Wato Rarara Kahutu.
Kafin Komawarta Karkashin Kamfanin Na Mawakin, A Baya Ana Yawan Ganinta Da Mai Shirya Fina Finan Nan. Abubakar Bashir Mai Shadda, Inda Bayan Auren Na Mai Shadda Ne Kwatsam Sai Akaga Ta Koma Bayan Mawaki Rarara Kahutu.
Hakan Yasa Mutane Su Fara Zargin Cewa Kamar Akwai Soyayya Mai Karfi A Tsakaninsu. Ta Yanda Ko Da Yaushe Ake Ganinsu A Tare.
Shin Akwai Soyayya Ne TsakaninKa Da Jaruma Aisha Humaira?
Wannan Itace Tambayar Damai Gabatarwa Ta Mishi A Cikin Shirin. Inda Mawakin Ya Bada Amsa. Ga Abin Da Mawakin Ke Cewa A Wanann Bidiyon.
https://youtu.be/bB71DBW2NrY