Na kashewa Ummita Naira miliyan dari da saba’in 170M – dan china da ake zargi ya kashe ummita
A yau din ranar laraba kamar yadda ake cikin Shari’a da Wani dan china da ake zargi da kashe wata budurwa mai suna ummita inda yau 16/11/2022 anka koma kotu domin cigaba da shari’arda ake da shi majiyarmu ta samu wannan bayyani da Abba Gwale ya wallafa a shafinsa inda ya bada labarin yadda shari’ar ke tafiya.
A zaman kotun da akayi a yau, lauyan dan China ya bayyana cewa dan China har garin su, Sakoto yaje sau uku yana gaishe da iya yenta tare da yi musu kyaututtuka , sun kuma shafe shekara biyu tare da Ummita.
Amma mahaifiyar Ummita ta ce sau daya ta san yaje sokoto.
Lauyan dan China ya tambayi Kanwar Ummita cewar ko tasan dan China ya kashe wa Ummita kudi miliyan dari da saba’in, ya ce ya kuma saka mata wani tallafi da yake bata dubu dari duk sati , Haka kuma ya taba shirya wa Ummita bikin birthday da a kashe kudi sama da dubu dari bakwai da saba’in.
Ya kuma siya mata gwala-gwalai na sama da naira miliyan uku da dubu dari uku a watan mayu na shekarar da muke ciki.
Sai dai Kanwar Ummita tace bata san ya yiwa Ummita wadannan abubuwan ba kawai tasan ‘yan uwansu ne basa son auren Ummita da dan China.
Wani labari Dalilin da ya sa na cinna wa ƴaƴana biyar wuta – Dattijo mai shekara 64
Joseph Ojo, mai shekaru 64, ya bayyana dalilin da ya sa ya kona ’ya’yansa guda biyar.
Ojo, wanda aka kama shi a hedikwatar ‘yan sandan Najeriya da ke Akure, jihar Ondo, ya bayyana cewa ‘ya’yan nasa ne suka hada da mahaifiyarsu domin su yi masa duka
Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa matarsa da ’ya’yan ango na cikin halin kashe shi da yunwa, duk da cewa ita ce ke bayar da kudin ciyar da shi.
A cewarsa, lamarin ya fusata shi, bayan da ya zaro mai daga chainsaw dinsa (na’urar yanka) ya zuba a dakin yaran kafin ya kona shi.
A ranar Asabar din da ta gabata ne Ojo ya banka dakin da ‘ya’yan ango ke kwana da wuta a gidansa da ke Fagun, cikin garin Ondo, hedikwatar karamar hukumar Ondo ta Yamma.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Funmi Odunlami, ta bayyana cewa uku daga cikin yaran biyar sun mutu sakamakon raunukan da suka samu a lamarin.
Odunlami ya kara da cewa Ojo ya ajiye tagwayen sa a wani daki kafin ya aiwatar da wannan aika aika.