Murna ta koma ciki: Yadda amarya da ƴan uwanta su ka tsere da N1.6m ɗin ango ranar aurensu
Wani ango daga Miliyan wanda amaryarsa ‘yar Khanewal ta danfare shi inda ta tsere da kudinsa mai yawa a ranar Juma’ar da ta gabata, dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
Angon mai suna Makhdoom Rasheed, ya bayyana wurin aurensa a yankin inda ya gane cewa amaryarsa da ‘yan uwanta sun tsere.
Angon ya bayyana yadda ya biya dangin amaryar Rs300,000 wanda yayi daidai da Naira miliyan daya da duba dari shida, yayin da ake shirin kulla alaka tsakaninsu.
A shekarar da ta gabata ma an samu bayani akan yadda wani ango ya tsere ba tare da ya ba amaryarsa hakuri ba a ranar aurensu.
Labarin angon mai sunan Kallum Narton ya bazu a duniya wanda ya ki bayyana a ranar aurensa a ranar 15 ga watan Satumba. Lamarin ya faru ne a Wales da ke UK.
WANI LABARI :Allah kada ya bani haihuwa koda Nayi Aure cewar wata Budurwa ya jawo cece kuce
Wata mace wadda ta amsa sunan ta mace ta kowace fuska, ta fitar da wani bidiyon ta tana mai bayyana wani sharadi ga duk namijin da ya yadda zai aure ta.A cewar ta tana so tayi aure, amma bata son yaya bata son ta haihu, ko da kuwa da daya ne.A cewar ta yaya wahala ce zalla samun su a rayuwa, saboda kula da su, dawainiyar su, basu tarbiyya, na daga cikin abinda ya sanya kwata kwata bata sha’awar su
.”Ina mamakin matan dake zumudin aure domin su Haihu, wata tace tana son yaya 3, wata 9, wata goma sha, mhn Ni tab ko daya bana sha’awa.”
Wai to da suke son ya’yan sun manta da dawainiyar su, basu kulawa, gaskiya bana sha’awar samun su kwata kwata.”
Dama sai na gayawa duk wanda zan aura cewa Ni fah bana sha’awar haihuwa, kuka ba zan haihu ba, saboda ban shirya wannan wahalar ba.”