Labarai

Miji Ya Kai Matarsa ​​Kotu Saboda Ta Auri Wani Mutumin A Ɓoye

Advertisment

Mista Ora, a cikin takardar ƙorafin da ya shigar, ya ce, “matata ta bar gidana ba tare da ta sanar da ni ba. Da na same ta kuma, sai ta furta cewa ta auri wani mutum daban. A kan haka ne na ke neman raba auren da ke tsakaninmu,” in ji shi.Miji Ya Kai Matarsa ​​Kotu Saboda Ta Auri Wani Mutumin A Ɓoye

Ya shaida wa kotun cewa surukar sa na hana shi zuwa domin yaga ɗansa. An sanar da ni cewa ɗana yana tare da surukata, sai na je na duba shi, amma surukata ta ƙi ba ni damar ganinsa.

Ta sha alwashi cewa ko zan gan shi, sai in ta mutu. Inda yace Ina roƙon wannan kotu mai daraja da ta raba auren ta kuma ba ni ikon riƙe ɗana. Alƙalin kotun, Labaran Gusau, ya ɗage ci gaba da sauraren ƙarar har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba.

Wani labari Ya ce min shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

Wata Matashiya a Najeriya ta bayyana irin halin da wata kawarta ta shiga bayan wani damfarar kalamai da wani saurayi ya yi mata lokacin suna nema.

Matashiyar mai suna Fairy Gbemie ta bayyana cewa mijin kawarta ya sharara mata karyar cewa shi dillalin motoci ne, to amma bayan sun yi aure ta gane cewa ashe Makanike ne.

Ko da yake bata bayyana sunan kawar ta ba, amma bisa la’akari da Kalamanta ta nuna cewa yana zirga-zirga cikin motoci daban-daban lokacin da yake zuwa wurin ta.

Duk da cewa har kawo yanzu ba ta bayyana tsawon lokacin da suka shafe a tare ba, amma galibin jama’a na hasashen cewa wannan aure ba lallai ne ya yi ƙarko ba.

Da ma dai a irin wannan zamani yan mata da dama na kasancewa ne a sahun ma’abota samun wurin hutu a rayuwarsu ta aure, to amma an ce tabbas idan da kwadayi lallai akwai wulakanci.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button