Labarai

Miji Da Mata sun kashe mai Gidansu Da sunkayi Garkuwa da shi bayan karba zunzurutun kudi ₦15M

Abeokuta – Jami’an yan sanda a jihar Ogun sun damke Miji da Matarsa da wani abokinsu kan zargin kashe wani attajiri kuma mammalakin Rolak Hotel, Otunba Abayomi Ajayi Smith.

Miji Da Mata sun kashe mai Gidansu Da sunkayi Garkuwa da shi bayan karba zunzurutun kudi ₦15M
Miji Da Mata sun kashe mai Gidansu Da sunkayi Garkuwa da shi bayan karba zunzurutun kudi ₦15M

Mijin mai suna Larry Adebayo Adewumi da matarsa mai suna Okereke Olufunmilayo tare da wani Adebowale Sanni sun hallaka attajirin bayan karban kudin fansan N15m daga hannun iyalinsa.

Sun aikata wannan aika-aika tun Satumban 2020 a Anifowose Estate dake Igbeba, Ijebu Ode amma sai yanzu asirinsu ya tonu, rahoton legit.

Bayan shekara biyu da kashe attajirin, a Satumban 2022 suka sake kitsa yadda zasu yi garkuwa da matarsa da ‘yayansa, hukumar yan sandan jihar ta bayyana.

Tace:

A Satumba, rundunar SP Taiwo Opadiran sun samu labarin ana sake shirin garkuwa da matar marigayi Ajayi Smith da yaransa.”

“Bincike ya kai ga damke wani
Adebowale Sanni a Ikeji Arakeji dake jihar Osun. Ya tona asirin yadda suke bibiyar matar marigayin, Yeye Olusola Roseline Ajayi Smith.”

Ya bayyana cewa Marry ne ya basu bayanan inda dakin Otal dinsu yake da kuma umurnin cewa idan suka samu nasarar sace matar da yaron su kashesu bayan karban kudin fansa kamar yadda suka yiwa mijin shekaru biyu da suka gabata.

An kama mata da mijin
Hukumar ta kara da cewa hakan ya sa suka kai simame damke Larry da matarsa.

Tace:

Bincike ya nuna cewa Larry dan damfara ne amma ya koma garkuwa da mutane. Ya samu bayanan Otunba Ajayi Smith daga wajen matarsa Olufunmilayo wacce ke yiwa attajirin aiki.”
Larry na da asusun banki biyu inda yake ajiye kudaden fansa. A asusun farko mai lamba 0010913206 dake bankin Jaiz, yana da milyan N34,953,455, yayinda aka samu milyan hudu (N4,576,846) a wani asusun na Access Bank.”

Kwamishanan yan sandan jihar CP Lanre. S. Bankole, ya jinjinawa jami’ansa bisa wannan nasara kuma ya umurcesu su binciko sauran mambobin gungun.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button