Lilin baba Ya Karyata Batun cewa Matarsa Ummi Rahab ta Bayyana tana da ciki, Yayi damarar Shiga Kotu
Fitaccen Mawakin nan Shuaibu Lilin baba yayi damar shiga kotu Sakamakon karya da akayiwa matarsa cewa tana dauke da juna biyu bayan kuma ba itace ta bayyana hakan ba.
Labarin dai ya karade Shafukan sada zumunta cewa ita ta bayyana tana da ciki ashe karyane , hakan yasa yace zai kai kara kotu.
Abinda yasa muma shafin hausaloaded munka dauki wannan labari duba da ganin yadda shafin fim magazine sunka tabbatar da hakan anan shafinsu na yanar gizo nan ne munka shiga bincike sai munka samu wani shafin Instagram mai suna Matar lilin baba wanda shafin fim magazine nayi repost nan ne munka samu kwarin gwirar cewa tabbas to yana yiyuwa sabon account dinta ne domin wannan hujja.
Amma a yau Majiyarmu ta samu wani sahihin labarin wanda tashar YouTube mai suna tsakar gida wanda shima yana cikin harka Masana’antar kannywood din ya samu tattaunawa da mijin ummi rahab wato lilin baba.
Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance a cikin sautin kiran wayar salula.