Koda Zan Yarda Ayi Sulhu Sai Ya Tara Yan Jarida Ya Karyata Kan Sa – cewar Hadiza Gabon
Kamar yadda sani akwai Shari’ar da tsakanin wanda yace hadiza Gabon ta canye masa kudi da cewa zata auresa amma daga baya ta musanta haka to yanzu nan majiyarmu ta samu wani labari wanda shafin dimokuraɗiyya na wallafa a shafin na Facebook cewa.
Kafin yanzu Bala Usman, ya Maka Jarumar Kannywood Hadiza Gabon a Kotu kan cewar ta karbe masa kudade da yawan su ya Kai ne dubu Dari uku da chasa’in da bakwai, bisa yarjejeniyar Aure daga bisani Kuma tace bata San zancen ba.
Shariar da alkalin Kotun (Court one) dake Magajin gari a kwaryar Jihar Kaduna, Rilwanu Kyautai, ke jagoranta.
An kwashe watanni ana gwabza Shariar, sai dai ita Jarumar ta karyata batun inda tace ita kwata-kwata bata San shi ba, bare har ayi Maganar ta karbe masa kudade.
Sai dai a zaman da aka yi ranar talata, wani babban lauya ya bayyana a gaban Kotun inda ya roki alkali cewar yana so zai shiga tsakiya domin sasanta tsakanin bangarorin guda biyu, Kuma alkalin ya basu dama har ma suka dibi adadin makwani biyu.
Da alama Jarumar Hadiza Gabon, bata ji dadi Maganar sulhun ba, hakan ya Saka ta fita daga harabar Kotun tana Surutai.
Bayan kammala zaman Lauyan Hadiza Gabon, ya bayyanawa Jaridar Dimokuradiyya, cewar shi sulhu alkairi ne to amma inda har zaa yi sulhu dole sai Bala Usman, Wanda yayi Kara ya tara Yan’jarida ya wanke Jarumar tare da tabbatarwa da duniya cewar baa asusunta yake zuba kudaden ba, tunda ya gaza kawo shedu a gaban Kotu.