Kaji Rabo : Kane ya ɗirkawa Amarya Yayansa Ciki
Da ɗumi-ɗumi: Wani Ƙani ya dirƙawa matar yayansa Amarya sabuwa fil ciki a Nasarawa.
Ƙani mai suna David, ya dirƙawa matar yayansa ciki a ƙaramar hukumar Doma Jihar Nasarawa. bayan yayan nasa ya tafi samun horo na wata tara domin zama Ɗan sanda.”
Rahoton ya cigaba da cewa, yayan na sa mai suna “Japhet” ya yi sabuwar amarya inda suka yi alƙawarin ba za su kusanci juna ba har sai ya dawo samun horo na zama cikakken Ɗan sanda.”
Bayan tafiyar “Japhet” ɗin zuwa samun horo ba wuya na zama Ɗan sanda, sai ƙaninsa “David” ya Yi amfani da wannan damar na wurin maye gurbin yayansa ɗin suna goge raini tsakaninsa da matar yayansa ɗin inda har sai da ta ɗauki ciki.”
Bugu da ƙari bayan dawowar “Japhet” jihar Nasarawa zuwa gida a domin duba iyali kawai sai yayi kaciɓis da wannan mummunar lamari, matarsa ɗauke da ciki rugum har na wata tara, biyo bayan tsananta bincike da aka yi bayanai suka tabbatar cewa ƙaninansa ne “David” ya dirƙawa mata ciki.”
Wani labari : Murna ta koma ciki: Yadda amarya da ƴan uwanta su ka tsere da N1.6m ɗin ango ranar aurensu
Wani ango daga Miliyan wanda amaryarsa ‘yar Khanewal ta danfare shi inda ta tsere da kudinsa mai yawa a ranar Juma’ar da ta gabata.
Angon mai suna Makhdoom Rasheed, ya bayyana wurin aurensa a yankin inda ya gane cewa amaryarsa da ‘yan uwanta sun tsere.Angon ya bayyana yadda ya biya dangin amaryar Rs300,000 wanda yayi daidai da Naira miliyan daya da duba dari shida, yayin da ake shirin kulla alaka tsakaninsu.
A shekarar da ta gabata ma an samu bayani akan yadda wani ango ya tsere ba tare da ya ba amaryarsa hakuri ba a ranar aurensu.
Labarin angon mai sunan Kallum Narton ya bazu a duniya wanda ya ki bayyana a ranar aurensa a ranar 15 ga watan Satumba. Lamarin ya faru ne a Wales da ke UK.