Har mata 150 sun kawo kansu, Matashin da ya bada sharuɗɗa 10 wanda sai mace ta cika zai aure ta
Wani matashi mai suna Solomon Hangega ya bayyana jerin abubuwan da yake bukata a wurin matar da yake son aure a wata wallafa da yayi a Facebook, Legit.ng ta ruwaito.
A wallafar yayi a wani rukunin Facebook mai suna Ukum Sons and Daughters Connect Worldwide, Solomon ya ce yana son hadaddiyar mace ta aure.
Ya ce wajibi ne mahaifiyar matar da zai aura ta kasance mai aikin jinya love lakcara. Kamar yadda yace, wajibi ne ta kasance daga Logo, ukum, Gboko ko kwande.
Akalla tana da ND a ganni lafiya ko BA ko BSc a wani babban fanni, banda shari’a ko jarida. Yace wajibi ne mahaifinta ya zama hamshakin dan siyasa kuma mai arziki.
A cewarsa yanzu haka ya samu mata wurin 150 da ke su ka cika duk sharuddan da yake nema a Facebook kadai.
Yayin da wasu kuma ke ta caccakarsa tare da zaginsa. Ya ce wajibi ne macen ta zama mai kugu madaidaici, albarkar kirji madaidaici, kyau, fata mai kyau, fararen idanu da sauransu