Labarai

Giyar Mulki ta Sanya Aisha Buhari ta umurci babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya gurfanar da dalibin Najeriya a Kotu kan rubutun da ya wallafa a Twitter

Majiyarmu ta samu wannan labari daga kafar sadarwa ta Facebook a shafin Daily True hausa inda sunka wallafa a shafinsu na sada zumunta.

An umurci Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, da ya gurfanar a gaban kotu, dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, Aminu Adamu Muhammed, wanda aka kama shi a shafinsa na Twitter cewa matar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha tana cin kitse da Kudin talakawa. SaharaReporters ta tattaro.

Giyar Mulki ta Sanya Aisha Buhari ta umurci babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya gurfanar da dalibin Najeriya a Kotu kan rubutun da ya wallafa a Twitter
Giyar Mulki ta Sanya Aisha Buhari ta umurci babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya gurfanar da dalibin Najeriya a Kotu kan rubutun da ya wallafa a Twitter

A cewar wani babban jami’in ‘yan sanda, A’isha ta bukaci ‘yan sandan da su daina musgunawa Muhammed amma ta dage cewa dole ne a gurfanar da shi a gaban kotu.

“An kai dalibin gaban IGP Baba Usman yau (Litinin) a hedikwatar rundunar,” majiyar ta shaida wa SaharaReporters.

“Za a gurfanar da shi a gaban kotu; Aisha ta dage cewa dole ne a kai shi kotu domin ya bayyana yadda (Aisha) ta wawure kudi. Ta ba da umarni ga IGP cewa dole ne a gurfanar da yaron a kotu.”

SaharaReporters tun da farko ta ruwaito cewa Muhammed, dalibi a shekarar karshe a Sashen Kula da Muhalli da Dabbobi, a watan Yuni 2022 ya wallafa a shafin Twitter cewa ba zato ba tsammani Misis Buhari ta kara nauyi bayan ta shiga cikin wawashe albarkatun kasa yayin da talakawa suke shan wahala karkashin mulkin mijinta.

Matar shugaban kasa ta shahara da tafiye-tafiye zuwa Dubai.

A Tweet din da yaron ya buga da Hausa yana cewa: “Su mama anchi kudin talkawa ankoshi.”

Kamar yadda abokansa suka bayyana, ya yi wannan furucin ne saboda ya ji takaicin yajin aikin da jami’o’in kasar suka dade suna yi.

Yajin aikin ya fara ne a watan Fabrairun 2022 kuma ya ƙare a watan Oktoba bayan watanni takwas.

Sai dai a ranar 8 ga watan Nuwamba jami’an tsaro suka dauke Muhammed mai shekaru 23 a harabar jami’ar inda aka ce an yi masa duka bayan kama shi da tsakar rana.

Ba a ba shi damar yin hulɗa da danginsa ko kuma lauya ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button