DA DUMI-DUMI: An garzaya da Aisha Buhari asibiti
Rahotanni daga fadar shugaban kasa na bayyana cewa an garzaya da matar shugaban kasa Aisha Buhari asibiti a Abuja a sakamakon karaya da ta samu a kafar ta
Majiyar Taskar Labarai Daily Nigeria ta ruwaito cewa ba asan musabbabin karayar ba amma dai “matar shugaban kasar ta zame ta fadi ne lamarin da ya jawo ta samu karaya a kafarta”
Sai dai kawo yanzu babu sanarwa a hukumance game da cikakken labarin abunda ya faru
Wani labari Kalli zafaffan Hotunan Kafin Aure Na Halima Atete Da Angonta
Masha Allah kamar yadda munka kawo muku labarin auren jaruma halima Atete a yanzu nan majiyarmu ta samu wasu zafaffan hotunan bikin daga shafin Bbchausa.
Halima Atete za ta shiga daga ciki
Tauraruwar Kannywood Halima Yusuf Atete tare da angonta Mohammed Mohammed Kala wadanda za a daura aurensu ranar Asabar 26 ga watan Nuwamban 2022 a Maiduguri.
Allah Ya sanya alheri
Kalli hotunan a NAN