Labarai

Biloniya Otedola Ya Gwangwaje Diyarsa da Kyautar Gidan N2.6bn Yayin da ta Cika Shekaru 30

Legas – Biloniyan ‘dan kasuwan Najeriya, Femi Otedola, ya girgiza diyarsa Florence wacce aka fi sani da DJ Cuppy bayan ya gwangwaje ta da kyautar gida mai kimar £5,000,000 wanda yayi daidai da N2.6 biliyan a kudin Najeriya, jaridar TheCable ta rahoto.

Fitacciyar diyarsa ta cika shekaru 30 a duniya a ranar Juma’a, ta bayyana kyautar da ta samu daga mahaifinta inda ta fitar da hirar da suka yi da biloniyan ‘dan kasuwan.

Biloniya Otedola Ya Gwangwaje Diyarsa da Kyautar Gidan N2.6bn Yayin da ta Cika Shekaru 30
Biloniya Otedola Ya Gwangwaje Diyarsa da Kyautar Gidan N2.6bn Yayin da ta Cika Shekaru 30
Ina alfahari dake diyata, Otedola

A hirar da suka yi, Cuppy ta zargi mahaifinta da mantawa da ranar da ta cika shekaru 30 a duniya wanda yayi martani da cewa hakan ba zai taba faruwa ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya kara da sanar mata cewa, ya umarci wani mai suna Andy a bankin Barclay da ya siya mata gida mai kimar £5,000,000.

Hakazalika, biloniya Otedola ya bayyana cewa ba zai iya tunanin wata kyauta da ta dace ya bata ba saboda a koda yaushe yana alfahari da ita.

Wani ya bani kyautar Rolex, Cuppy

A daya bangaren, Cuppy ta je shafinta na Twitter inda ta bayar da labarin wani matashi da baya birgeta amma ya siya mata kyauta mai tsada domin murnar ranar zagayowar haihuwarta

Ta rubuta:

Wannan gayen ya siya min agogo Rolex kuma har yanzu bani da lokacin shi.”

Femi Otedola ya cika shekaru 60 a duniya

Legit.ng ta rahoto muku cewa fitaccen ‘dan kasuwar mai Femi Otedola ya cika shekaru 60 a duniya inda ya fitar da zunzurutun kudi yayi hayar jirgin ruwa.

Shi, iyalansa da abokan arziki zasu kwashe makonni uku suna zagaye da yawon shakqara a jirgin ruwan duk a cikin shagalin zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button