AddiniLabarai

Babu abinda zai hana yi yiwa yan takara Addu’a – Alaramma Ahmad Suleiman Kano

Advertisment

Shigar da muke yi harkokin siyasa ta taimaki ci gaban addinin Musulunci a arewacin Nijeriya in ji Alaramma Ahmad Suleiman a cikin hira.

Babu abinda zai hana yi yiwa yan takara Addu'a - Alaramma Ahmad Suleiman Kano
Babu abinda zai hana yi yiwa yan takara Addu’a – Alaramma Ahmad Suleiman Kano

A cikin wannan hirar da jaridar dcl hausa suke da babban alaramma da ke jan baki alaramma Ahmad Suleiman kano akan anga malam ya shiga harka siyasa wanda yana yiwa yan takara Addu’a da kuma zuwa wajen yakin neman zabe kamfin kenan inda anka hango hoton malam a jihar plateau jos da APC nayi a wannan sati, ga yadda hirar ta kasance.

Mai Tambaya: miyasa yanzu ake ganin malam wajen yakin neman zabi.

Alaramma: “Assalamu warahamatullah wabarakihu lallai na dade ina abubuwa na siyasa na fara harka siyasa tun lokacin da anka ƙirkir APP kafin ta zamo jami’yar ANPP tana APP nayi takarar chairman a lokacin bayan ina bin yan siyasa nan zaka ga nabi sule lamido Jigawa kamfen Sa’a nan nazo kano yaje kamfen din neman zaben Ganduje tenuwarsa ta farko hakama ta biyu.

Shine wannan karo ake ta nema na musamman a jamiyun nan biyu na fara shiga gidan Atiku daga baya naga akwai yar damuwa kadan na sake ra’ayi na dawo APC yanzu haka duk abinda na fara a sabon abu bane idan kazo kano zakaga ina bude taro da addu’a haka lokacin kwankwaso na rike wasu yan mukamai na rike chairman masu bada shawara a wata ma’aikata shekara goma sha biyu 12 daga baya anka bani commissioner 2 a ilimin bai daya a kano wanda yanzu haka ina rike da wannan mukami.

Mai Tambaya : wane irin abubuwa malam ke dubawa kafin goyon bayan dan takara?

Alaramma:

Alaramma: abinda nake dubawa tsakanina da Allah  alamun idan wannan mutum yaci  al’umma zasu ci-gaba  kuma  kada a tabi addinin Musulunci wato kuma kada ayiwa addinin musulunci zagon kasa kar a cutar da addinin musulunci  kuma yazamana za’a amfani mutane wannan shi nake sawa ya zamo motive dina nabi mutum dan siyasa.

Alaramma: abinda nake dubawa tsakanina da Allah  alamun idan wannan mutum yaci  al’umma zasu ci-gaba  kuma  kada a tabi addinin Musulunci wato kuma kada ayiwa addinin musulunci zagon kasa kar a cutar da addinin musulunci  kuma yazamana za’a amfani mutane wannan shi nake sawa ya zamo motive dina nabi mutum dan siyasa.

Mai Tambaya: shin shigarku harka siyasa kwaliyya ta biya kudin sabulu an samu cigaba a gefen addini?

Alaramma: eh Alhamdulillahi ana samu yadda zakaga daman harka siyasar ta Nijeriya babu provision na harka addini inda zaka gane an samu cigaba sai ka koma baya a lokacin gwamnan Zamfara ya kirkiri ko ya jaddada wanda jahohi da yawa sunka jadadda Sa’a nan anka samu hukumomi irinsu hisbah wanda suke kari martabar addini da al’adu wannan cigaba ne da anka samu a cikin Addini ‘.

Yanzu misali a jihar kano akwai wani program da Ganduje ya kirkira na musuluntar da maguzawa.’

Ga bidiyon nan domin saurarin cikakkiyar hirar da ankayi da alaramma.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button