Kannywood

APC ta saka ƴan Kannywood a kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu

Darakta-Janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Gwamna Simon Lalong, ya amince da shigar da ‘yan Kannywood cikin kwamitin.

Lalong, wanda kuma shi ne gwamnan Plateau, ya sanar da amincewar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dr Makut Maham, ya fitar a yau Talata a Jos.

APC ta saka ƴan Kannywood a kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu
APC ta saka ƴan Kannywood a kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu

Ya ce shigar da su wani bangare ne na kokarin zurfafa shigar da masu fasaha daga shiyyar Arewa a yakin neman zaben.

Dailu Nigerian ta rahoto cewa Babban daraktan ya ce amincewar ta biyo bayan ziyarar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu ya kai Kano, inda ya gana da ‘ya’yan kungiyar.

Ya ce, Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa an baiwa ‘yan Kannywood damar shiga cikin yakin neman zabe domin baje kolin basirarsu, tare da taimakawa jam’iyyar ta samu nasara a zabukan dake tafe.

Lalong ya dora wa kungiyar alhakin hada kai tare da fadakar da dimbin mabiyansu a kan tallan Tinubu da kuma manufofinsa domin yi masa ruwan ƙuri’u a ranar zaɓe.

Sanarwar ta ce, kungiyar ta Kannywood ta na da Abdul-Mahmud Amart a matsayin Darakta, Ismail Afakallah a matsayin mataimakin darakta da Sani Mu’azu a matsayin sakatare, tare da sauran shugabannin da ke jagorantar bangarori daban-daban.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button