An zaɓi mace musulma ‘yar majalissar jiha a Amurka
Ita ce mace musulma mafi ƙarancin shekaru a ciki
Majiyar mu ta The Islamic Info ta ruwaito cewa Nabeela ‘yar shekara 23, bayan kasancewar ta mace musulma, haka nan kuma itace mafi ƙarancin shekaru a cikin ‘yan majalissun su 51 da aka zaɓa.
A washe garin zaɓen, wato ranar Laraba ne dai Nabeela ta wallafa saƙo na nuna murnar nasarar da ta yi a shafin ta na tuwita, inda ta nuna farin cikin nasarar ta a yankin da ‘yan Republican suke da ƙarfi duk da kasancewar ta ‘yar Demokrat (Democrats).
Matar ta kuma wallafa a shafin ta na Instagram cewa a lokacin da ta ƙuduri aniyar neman takarar, ta ɗauki salon shiga cikin jama’a don nusar dasu kan mahimmancin dimokuraɗiyya gami da nuna musu muhimmanci samun shugabanci na gari.
Ta kayar da ɗan takarar dake kan kujerar
Nabeela Syed dai ta doke abokin hamayyar ta na Republican wanda shine ɗan majalissa mai ci, mai suna Chris bos da kaso hamsin da biyu (52%) na ƙuri’un da aka kaɗa.
Bisa nasarar da Nabeela ta samu, ta zamto itace mace musulma ta farko da aka zaɓa a yankin na Illinois. Akwai wani namiji ɗan asalin Fasasɗin mai suna Abdelnasser Rashid wanda shima musulmi ne da yayi nasara a zaɓen da ya gabata.
Nabeela dai ta kasance mace musulma mai ƙoƙarin sanya hijabi a koda yaushe. An haife ta a yankin Palatine dake Illinois, kuma tayi karatukanta a jami’ar Kalifoniya a ɓangarorin kimiyyar siyasa da kuma harkokin kasuwanci.
Ance ta kasance mace ‘yar gwagwarmaya ce mai ƙoƙarin ƙwato ma waɗanda aka tauye ‘yancin su a yankin da ta fito. Ta taɓa riƙe shugabar wata ƙungiyar sa kai dake taimaka ma masu ƙananan sana’o’i da shawarwari.
Tayi alƙawarin kula da ɓuƙatun al’umma
A ƙudururrukan yaƙin neman zaɓen ta, Syed tayi alƙawarin maida hankali wajen yin abubuwan da suka jiɓanci hidindimun al’umma, musamman irin samun daidaito, ɓangaren kiwon lafiya, ilimi da kuma ɓangaren haraji.