A Taya Mu Da Addu’a Kan Tsare 442 A Nijar – Mahaifin Mr. 442
A cewar mahaifin mawakin, sun tura wani daga Najeriya don ya nemi belin Mr. 442 da abokinsa Ola.
Mahaifin mawaki Mr. 442, ya yi kira ga jama’a da su taya su da addu’a saboda tsare dansa da hukumomin Jamhuriyar Nijar suka yi.shafin voahausa na ruwaito
A farkon makon nan ne hukumomin Nijar suka tsare Mubarak Abdulkarim, wanda aka fi sani da Mr. 442 tare da wani abokin huldarsa da ake kira Ola.
“Muna neman addu’a daga wurin ‘yan uwa da abokan arziki, don wannan halin da yake ciki, don ya samu ya dawo gida cikin koshin lafiya.” Mahaifin 442, Alhaji Abdulkarim Idris ya ce.
Mahaifin mawakin ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom FM na Kano a ranar Laraba.
Mr. 442 da abokinsa Ola ‘yan asalin Najeriya ne, amma sukan shiga kasar ta Nijar domin gudanar da wasa.
Hukumomin Nijar na zarginsu da yunkurin yin faspo din kasarduk da cewa su ba ‘yan kasa ba ne.
Bayanai sun yi nuni da cewa mawakan sun gabatar da kansu a matsayin ‘yan kasar ta Nijar, lamarin da ya sa aka kama su bayan daka gano karya suke yi.
Sai dai mahaifin Mr. 442, ya dora laifin a kan wani abokin dansa da ke kasar ta Jamhuriyar Nijar.
“Wani abokinsa ne da suke can Nijar suka ce za su taimaka su mashi faspo na zuwa kasar waje, ashe takardun da suka mashi ba masu kyau ba ne.” In ji mahaifin 442.
Ya kara da cewa sun samu labari jakadan Najeriya ya kai musu ziyara, sannan su ma sun tura wani dan uwansu daga Najeriya zuwa Nijar don ya nemi belinsu.
Alhaji Idris dai ya ce, har sun samu zarafin ganawa ta waya da dansa, inda ya tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya.