Yadda Rarara Yaci mutuncin Gwamonin kano
Shahararren marubucin nan datti assalafy yayi wani rubutu inda ya nuna cewa Dauda Kahutu Rarara yaci mutuncin gwanonin jihar kano wanda duk sun taimakesa a rayuwarsa inda ya wallafa kamar haka.
“RARARA KENAN
Mawaki Dauda Kahutu Rarara mai abin mamaki
Yaci mutuncin Tsohon Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya kirashi da “DUNA”
Yaci mutuncin tsohon Gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya siffantashi da halittar biri “TSULA”
Yanzu mun wayi gari yaci mutuncin Gwamnan Kano mai ci Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kirashi da “SINQE” mai sankame kudin al’umma
A cikin wadannan shugabanni da wannan mawaki ya zage babu wanda bai taimakeshi ba, a dalilinsu ya samu arziki, ya saka musu da butulci
Shi dai Rarara dan jihar Katsina ne, ance almajiranta ya kawo shi Kano, gashi nan ya zage shugabannin Kano, kuma ba mai taka masa burki a cikin ‘yan gari
Allah Ya kyauta”
A Cìkìn Sabuwar Waƙar Dauda Kahutu Rarara Yayi Wasu Baitúka Kamar Haka
•Kace acire sunana wannan naji
•Dama bance asakani ba inda kaji
•Duk wani taro da kake kaina to naji
•Mu harkar tunubu ba saida takarda ba
•Shi dai zabo a sanina baya chara
•Ko a buga ko abari dai Nine Rarara
Na ari rigar gamji ko dan nai sara
•In dutse yakafu badai turewa ba
A ganin ku da yake a wannan baitukan da suke cikin sabuwar waƙar tasa ?
Ga wakar nan zaku iya Download ku saurara kuji..
MUSIC : Rarara – Lema Ta sha kwaya