Yadda Aka Kama Likita Yana Lalata Da Kanwar Matarsa A Daki
Wani labari wanda jaridar Premium Times Hausa ta rawaito ya tabbatar da cewa rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama shahararren likitan cutar daji Femi Olaleye da laifin yi wa ‘yar uwan matarsa fyade.
Olaleye wanda shine mai mallakin asibitin kula da masu fama da cutar daji ‘Optimal Care Centre’ dake Surulere a jihar Legas ya yi shekara daya da watanni 9 yana lalata da ‘yar uwar matarsa.
Uwargidan likitan Remi Olaleye wacce ita ce ta kai karar sa kotu ta ce ya ci mutuncin ta matuka.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benjamin Hundeyin ya ce rundunar ta aika da file din karar likitan zuwa fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka domin gudanar da bincike da shawara.
Likitan ya ki amsa kira da sakonnin tes da aka aika wayoyinsa kan zargin fyade da ake masa.